✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya rike numfashinsa tsawon minti 24 a cikin ruwa

Wani mai suna Budimir Buda Šobat mai shekara 54, ya kafa tarihin wanda ya fi kowane mutum dadewa a cikin ruwa ba tare da ya…

Wani mai suna Budimir Buda Šobat mai shekara 54, ya kafa tarihin wanda ya fi kowane mutum dadewa a cikin ruwa ba tare da ya yi numfashi ba, inda ya yi mintuna 24 da dakika 33 ba tare da ya fito daga cikin ruwan ba ko ya shaki iska.

Budimir wanda ya fito daga kasar Croatia, ya gudanar da hakan a wani tafkin ninkaya a birnin Sisak, a karkashin kulawar likitoci da manema labarai da wasu masu goyon bayansa, inda suka ga lokacin da ya shiga cikin ruwan.

Bayan daukar lokaci a cikin ruwan ba tare da numfashi ba, an saka masa iska don kara wa jininsa zagayawa ko’ina a jikinsa, kamar yadda ya saba, inda Budimir ya kai kusan rabin awa a kasan ruwan, ba tare da ya dago kansa ba.

Da farko lamarin ya kasance mai kamar wuya a samu wani mutum da zai iya yin hakan, sai dai wannan mutum ya kasance yana yin abubuwa masu matukar hadari wanda ya dauki tsawon shekaru biyu yana atisayen samun wannan kambu.

Shekaru kadan da suka wuce, Budimir ya nuna sha’awarsa kan wasan horon gina jiki, sannan ya fara atisaye a cikin ruwa wanda hakan ya sa shi cikin jerin mutum 10 da suka shahara a duniya.

A yanzu ya samu kambun wanda ya fi kowa dadewa a cikin ruwa bayan kwace kambun a hannun wanda yake rike shi shekara uku da suka gabata.

Ya samu kambun ne ta hanyar shiga cikin Kundin Tarihi na Duniya na Guinness, bayan kwashe minti 24 da dakika 11 a cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba.

Yayin fitowar Budimir daga ruwan da ya shafe minti 24 da dakika 33
Budimir tsaye a jikin agogon da ya rike lokacin da ya shafe a cikin ruwan

Wanda yake rike da kambun a baya mai suna Branko Petrobic, ya zama gwarzon ne bayan ya yi minti 11 da dakika 54 a cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba, kuma ya zama gwarzon ne a shekarar 2014 a birnin Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa.

A wannan karon Budimir Buda Šobat ya kwace kambun saboda tsawan lokacin da dauka a cikin ruwa ba tare da ya yi numfashi ba.

Bayan Budimir Buda Šobat ya yi minti 18 a kasan ruwa ya fara fuskantar wani irin sauyin yanayi a jikinsa, inda gabobinsa ba su samun kuzari, sakamakon rashin shakar numfashi da bai yi ba na tsawan lokaci.