✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya shiga hannu bayan yi wa karamar yarinya fyade

Mutumin ya far wa karamar yarinyar da misalin karfe uku na dare.

Dubun wani mai shekara 30 ta cika bayan ya yi wa wata karamar yarinya fyade.

An cafke shi ne bayan mahaifin yarinyar mai shekara 13 ya kai kara ofishin ’yan sanda cewa mutumin ya zakke wa ’yarsa da tsakar dare.

Binciken da ofishin ’yan sanda na yankin Ngor Okpala, Jihar Imo ya gudanar ya gano cewar lamarin ya faru a ranar 23 ga Mayu, 2021 da misalin karfe 3:33 na dare.

Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, SP Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an shigar kara kuma suna gudanar da bincike.

Alkana ya ce tuni aka garzaya da yarinyar zuwa asibiti don ba ta kulawa da kuma gudanar bincike ta fuskar harkar kiwon lafiya.