✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya ta kone iyayenta kurmus suna tsaka da barci a Legas

Ta kone su ne bayan ta dura musu kwayoyi suna tsaka da barci

’Yan sanda a jihar Legas sun fara bincike kan dalilin da ya sa wata mata mai shekara 52 ta dura wa iyayenta su biyu kwayoyi sannan ta kone su kurmus.

Bayanai sun nuna wacce ake zargin, Aleremolen Izokpu ta ba mahaifinta mai shekara 85, mai suna Michael Izokou da mahaifiyarta mai shekara 80 mai suna Priscilla, kwaya kafin ta banka musu wuta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ’Yan Sandan Jihar ta Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce lamarin ya faru ne ranar Larabar da ta gabata a rukunin gidaje na Lusada da ke unguwar Okokomaiko a hanyar Legas zuwa Badagry.

Ya ce mahaifin matar dai likitoci sun tabbatar da rasuwarsa, yayin da ita kuma mahaifiyar har yanzu ba ta cikin hayyacinta.

Benjamin ya ce, “Bayanan da muka samu daga Baturen ‘Yan Sandan Okokomaiko sun nuna lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Laraba, daya ga watan Disamba, 2022.

“A lokacin ne muka sami kiran gaggawa daga kanwar mamacin, wata mai suna Osemudiame Izokpu, cewa wata yayarta mai kimanin shekara 52 ana zarginta da dura wa iyayen nasu kwaya sannan ta kone su suna tsaka ba barci.

“’Yan sanda sun ziyarci wajen da lamarin ya faru da kuma asibitin da aka kai gawar, suka dauki hotonta sannan suka mayar da ita sashen adana gawarwaki na asibitin Badagry,” inji Benjamin.

Kakakin ya kuma ce yanzu haka suna ci gaba da bincike don ganin sun kama wacce ake zargin.