✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yanke marainansa yana cikin barci

Ni kaina bai san yadda aka yi na dauko wukar ba, abin ya daure min kai.

Wani manomi a kasar Ghana mai suna Kofi Atta ya iske kansa a asibiti a cikin wani mawuyacin hali bayan da ya yanke marainansa a lokacin da yake tsaka da barci.

Atta, ya shaida wa BBC a kan gadon jinya, yadda lamarin ya faru daki-daki, inda likitoci ke ta kokarin duba yadda za su yi masa aiki.

Ya ce a yanzu dai ana masa karin ruwa ne tare da wasu allurai, amma duk da haka sai an yi masa tiyata.

Ya kara da cewa a yanzu ba ya da ko kudin da zai biya motar asibitin da za ta dauke shi zuwa Asibitin Koyarwa na Komfo Anokye, da ke Kumasi a Ghana, inda a can ne za a iya yi masa babbar tiyata.

Mutumin ya ce, yana barcin da rana ne a kan wata kujera sai ya yi mafarki cewa yana yanka nama a ajiye a gabansa, wanda zai dafa abinci da shi, inda a cikin barcin ya janyo wuka ya yanke marainansa.

Atta, ya ce abin ya ba shi mamaki kwarai domin har lokacin da wasu makwabtansa biyu suka kawo masa agaji bai san me ya faru ba, sai da ya tashi daga kan kujerar ya rika jin wani zafi a gabansa ga kuma jini na zuba.

Mutumin ya ce, har lokacin da aka kawo masa daukin ba ya tabbacin abin da ya faru, ji yake kamar yana mafarki ne.

Ya ce shi kansa bai san yadda aka yi ya dauko wukar ba, “Abin ya daure min kai,” in ji shi.

Manomin mai shekara 47 wanda ke garin Assim Akomfode a Ghan, bayan ya yanke marainan nasa a cikin barci har ya yi kururuwar neman taimako bai farka ba yana cikin mafarki ne domin shi duk bai san abin da ya faru ba a lokacin.

Ya ce duk da cewa makwabtansa sun kai masa dauki inda ya rika jin zafi a gabansa ga kuma jini yana zuba, bai fahimci abin da ya faru ba, sai daga baya a gadon asibiti hankalinsa ya dawo ya gane abin da ya faru.

Karin haske daga likitoci A fagen ilimin kula da lafiya, akwai wata larura da ake kira ‘Parasomnia’ a Ingilishi, inda mutum kan aikata wasu abubuwa sabanin na hankali a lokacin da yake barci.

Wannan larura takan sa mutum ya rika tafiya ko maganganu ko fitsarin kwance ko mugun mafarki ko kikkifta ido da sauran abubuwa na daban a lokacin da yake barcin.

A lokacin da mutum yake cikin wannan hali wasu da ke tare da shi ko kusa da shi za su ga kamar ba barci yake ba yana farke ne, to amma yana cikin barci ne bai san abin da yake yi ba.

Mutanen da ke cikin wannan yanayi ba sa iya tuna abin da ya faru da su ko abin da suka aikata a lokacin da suke cikin haka.

Bayanai sun ce abin da mutum kan yi a wannan lokacin kamar yana aikata abin da mafarkinsa ya kunsa ne a zahiri.