✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi bidiyon tsiraici don nema wa Tinubu nasara

Olaiya Igwe ya wallafa bidiyonsa yadda ya yi zindir a bakin teku yana rokon dodannin teku su ba wa dan takarar sa'a

Tsohon fitaccen jarumin fina-finan Najeriya, Ebun Oloyede, wanda aka fi sani da Olaiya Igwe ya yi wa kansa tsirara, haihuwar uwarsa, don roka wa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, nasara a zaben 2023.

Fitatccen jarumin kuma mai shirya fim din, ya wallafa bidiyon yadda ya yi zindir a bakin teku yana rokon dodon cikin harshen Yarbanci ya ba wa Tinubu nasara.

“Ya ubangiji na zo gare ka ne saboda Bola Ahmed Tinubu; ina rokon ka ba shi nasara a zabe mai zuwa,” in ji Olaiya Igwe, a cikin bidiyon da ake ganin wani sabon salo ne na yakin neman zabe.

Tuni dai bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Juma’a ya karade kafofin sada zumunta, inda masu bayyana ra’ayinsu a kai suka yi masa ca.

An kuma ji shi a ciki yana cewa, “Na zo bakin teku ne musamman domin in roke ka, ka sa Tinubu ya samu kuri’u kamar yawan ruwan teku, kada ka sa mu kunyata.”

An yi wa Olaiya Igwe ca

A tare da bidiyon sai ya rubuta cewa, “Ina farin cikin goyon bayan dan takaran da ya dace da manufofinmu.

“Dan takara daye ne kawai zai cika mana burinmu ya kuma yi fadi-tashin cikin Najeriya zuwa mataki na gaba, shi ya sa nake goyon baya da kuma neman ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Jagaban ya zaman shugaban kasan Najeriya na gaba.”

Tun bayan fitar bidiyon da Olaiya Igwe ya yi a huntunsa masu amfani da kafofin sada zumunta ke ta bayyana ra’ayoyinsu.

Fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen rediyo, Dotun, ya bayyana takaicinsa, ta shafinsa na Twitter, ya ce, “Fitowar Olaiya Igwe tsirara haihuwar uwarsa a bidiyo abin kyama ne.

“Ba laifi ba ne ya goyi bayan duk wanda ya ga dama, amma hatta wanda kake goyon baya zai yi takaicin wannan abin, ya kamata ka nuna dattaku; Wannan ya fi kaskanci kaskancewa,” in ji Dotun.

Wani mai amfani da Twitter, @IamDukeilorin. “Na kasa daina dariyaBabu wanda ya ce kada Olaiya Igwe ya yi wa wanda yake goyon baya addu’a, amma abin kyama ne ka yi bidiyon kanka tsirara sannan ka yada kowa ya gani a kafofin intanet.”

Wasu kuma addu’ar neman sauki  suka rika yi wa Olaiya Igwe, domin a cewarsu, yana neman addu’a.

Olúyẹmí Fásípè AICMC, with the Twitter handle, @YemieFash, ya ce, “Ina tausaya wa Olaiya Igwe, kan wannan hali da ya shiga. Ina masa addu’a Allah Ya dawo da shi cikin hayyacinsa.”

Wani kuma, Adenekan Mayowa, @Mayorspeaks, da yake bayyana takaicinsa ya ce, “Olaiya Igwe da muka taso muna girmamawa shi ne ya mayar da kansa abin dariya. Allah Ka rufa mana asiri da wadata har bayan mun dainda aiki.”