✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya yi wa ’yar shekara 80 fyade

Rahotanni sun ce mutumin ya shiga dakin tsohuwar ne ta taga.

A jihar Ondo, an kama wani mutum mai shekara 50 bisa zargin ya yi wa wata tsohuwa mai kimanin shekara 80 fyade.

’Yan sanda sun kama mutumin, mazaunin garin Akure na Jihar wanda ya yi ikirarin fitowa daga gidan yari a kwanan nan, bisa aikata aika-aikar a kan tsohuwar.

Rahotanni sun ce mutumin ya shiga dakin tsohuwar ne ta taga inda ya yi mata barazana da diga sannan ya yi mata fyaden.

Wata makociyar tsohuwar, mai suna Julianah ta ce mutumin ya shiga dakin tsohuwar da karyar cewa zai karbi wani jikon magani ne a gurinta.

Ta ce kukan tsohuwar ne ya ankarar da mutane inda suka balle kofar dakin sannan suka tarar da shi tsirara.

Rahotanni sun ce daga bisani ’ya’yanta sun sake mata matsuguni daga unguwar saboda cin zarafin.

Sai dai mutumin ya nemi tsohuwar da ta yafe masa, yana mai cewa bai dade da fita daga gidan yari ba.

Ya ce, “Ban san mene ne ke damuna ba. Kwanan nan aka sako ni daga gidan kurkuku.

“An daure ni ne saboda aikata laifi makamancin wannan.

“Na kasance ina aikata fyade na tsawon lokaci.

“Don Allah a yafe mini,” inji shi.

Sai dai da Aminiya ta tuntube shi, Kakakin ’Yan Sandan Jihar ta Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro, ya ce sata ake zarginsa da aikatawa ba fyade ba.

A cewarsa, da gaske ne mutumin yana da kuruciyar bera musamman satar wayoyin dattijan mutane kuma an kama shi yana aikata hakan inda aka yi masa dukan tsiya.

Jami’in ya ce an mutumin yana hannun ’yan sanda kuma an fara gudanar da bincike a kansa.