Ya zama wajibi Jamus ta ba wa Ukraine makamai —Scholz | Aminiya

Ya zama wajibi Jamus ta ba wa Ukraine makamai —Scholz

Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz
Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Scholz
    Ishaq Isma’il Musa

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wajibi Berlin ta kara wa Ukraine makamai don kare kanta daga barazanar dakarun Moscow.

Gidan Rediyon Jamus ne DW ya ruwaito Scholz yana bayyana hakan ne yayin da yake jaddada matsayar gwamnatinsa na hana Rasha cimma burinta na mamaye Ukraine.

Olaf Scholz ya gayawa majalisar dokokin Jamus ta Bundestarg cewa, gwamnati na tattaunawar sirri da hukumomin Kyiv game da yiwuwar tabbatar da tsaro ga barazar da Moscow ke yi wa Ukraine

Gwamnatin Ukraine ta nemi agajin tsaro daga kasashen Turkiyya da China da Jamus, bayan da Rasha ta hana ta zama mamba a kungiyar hadakar tsaro ta NATO.

A makon nan ne Babban zauren Majalisar Dinkun Duniya ya kada kuri’ar dakatar da Rasha daga hukumar da ke kare hakkin dan Adam yayin wani zama da aka yi a birnin New York.

Matakin ya biyo bayan tuhumar da ake ma Rasha cewa sojojinta na aikata laifukan yaki a Ukraine.