✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yada bayanan ’yan ta’adda: Gwamnati za ta kafa wa BBC da Trust TV takunkumi

Gwamnati a ce kafafen biyu sun karya doka kuma dole a hukunta su

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kakaba wa gidan talabijin na Trust TV, mallakar Kamfanin Media Trust da kuma tashar BBC takunkumi saboda yada labaran ‘yan bindiga.

Kafofin da lamarin ya shafa dai sun yada shirye-shirye mabambanta da ke fallasa yadda harkokin ‘yan bindigar dajin ke jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Sa’ilin a yake magana da ‘yan jarida a ranar Alhamis, Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu Lai Mohammed, ya ce shirye-shiryen da aka yada din kara wa ‘yan ta’addan tagomashi suka yi a kasa.

Ya kara da cewa, hukumar da ke da hakkin kula da lamarin ta soma nazari kan batun kafin daga bisani ta kakaba wa kafofin biyu takunkumin da ya dace.

A cewar Ministan, “Akwai hukumar da ke kula da harkokin yada labarai, wato Hukumar Kula da Tashoshin Talabijin da Rediyo ta Najeriya (NBC), kuma tana sani da abin da ya faru.

“Suna nazarin bangaren dokar da BBC da Trust TV suka take. Harkar yada labarai tamkar iskar numfashi ce wadda da ita barayin daji da ‘yan bindiga ke amfani wajen numfasawa.

“Abin takaici ne yadda BBC suka bada kafarsu ga ‘yan ta’adda suna nuna fuskokinsu tamkar wasu jaruman fim.

“Ina mai tabbatar musu ba za su sha ba, za a kafa wa kafofin biyu takunkumin da ya dace,” inji Ministan.

Ya ci gaba da cewa, duk da dai BBC kafa ce daga ketare wadda ba ta karkashin kulawar NBC hakan ba zai hana kafa mata tankunkumi ba.

Ya ce, “Ina mai tabbatar muku ba za su sha ba daga daukakar da suke bai wa ‘yan bindiga da barayin daji a Najeriya. Idan kuwa shirye-shirye kawai suke watsowa alhali ba su da rijista a Najeriya, za mu fada musu su daina watsowa. Saboda akwai kasa mai suna Najeriya shi ya sa suke gudanar da harkokinsu a nan,” inji shi.