✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadd ake hada abun wanke bayan tukunya

A yau na kawo muku yadda ake hada abun wanke bayan tukunya (vim) a gida cikin sauki. Ana kuma amfani da shi wajen wanke butar…

A yau na kawo muku yadda ake hada abun wanke bayan tukunya (vim) a gida cikin sauki.

Ana kuma amfani da shi wajen wanke butar karfe ko goge duk wani abu mai tsatsa.

Ana fi amfani da shi wajen wanke bayan tukunya ne saboda yana fitar da tsatsa da bakin tukunya sosai.

  • Abubuwan hadawa:
  1. Bawon kwai
  2. Toka
  3. Omo
  • Yadda ake hadawa
  1. Da farko za a samu bawon kwai wanda ya bushe sosai a daka shi sosai a tankade.
  2. Sai a samu toka shi ma a tankade sai a hada da tankadaden bawon kwan.
  3. Sannan sai a zuba omo kadan a juyaya sosai.
  4. Wannan shine yadda ake hada vim a gida.

Da fatan zaa gwada a gani.