✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka cafke Nnamdi Kanu a kasar waje

Jami'an tsaron Najeriya sun taso keyarsa domin ya fuskanci hukunci.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce a kasar waje jami’an tsaro suka cafko shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Malami ya bayyana wa ’yan jarida cewa a ranar Lahadi, 27 ga watan Yuni, 2021, ne hadin gwiwar hukumomin tsaron Najeriya suka cafke Kanu, aka kuma tiso keyarsa zuwa Najeriya.

Malami wanda bai yi cikakken bayani kan kamen ba, ya ce “Kanu, wanda ya tsere bayan kotu ta bayar da belinsa domin kulada lafiyarsa, “An dawo da Najeriya domin ci gaba da fuskantar shari’ar da ake tuhumarsa da laifuka 11.

“Idan da za a tuna, ana tuhumar Kanu, wanda aka fara tsarewa a ranar 14 ga Oktoba, 2015 da aikata laifuka 11 da suka danganci ta’addanci da cin amansar kasa da jagorantar haramtacciyar kungiya da mallakar haramtattun makamai da fasakwauri da wallafa abubuwan cin mutunci da sauransu.”

Yadda Kanu ya tsere

Game da yadda aka yi har Kanu ya tsere da farko, Ministan ya ce, bayan da kotu ta bayar da belin Kanu domin kula da lafiyarsa, sai ya bijire ya ki sake halartar zaman kotu.

“A nan ne kotu ta bayar da sabon umarnin a kamo tama shi, tunda ya saba sharadin belin.

“Bayan tserewarsa sai ya ci gaba da amfani da kafafen talabijin da radiyo da intanet yana tunzura mutane su yi wa Najeriya da hukumomin kasar tashin hankali.”