✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka ceto masu Sallar Tahajjud da aka yi garkuwa da su

’Yan sanda sun ce kawo yanzu ba a san inda mutum 10 daga cikin masallatan suke ba.

An kubutar da mutum 30 daga cikin mutum 40 da ’yan bindiga suka yi gakuwa da su a yayin da suke yin sallar Tahajjud a wani masallaci a Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta ce an kubutar da masallatan ne bayan jami’an tsaro da ’yan banga da mutanen gari sun bi sawun ’yan bindigar, bayan samun labarin garkuwa da su a Unguwar Kwata da ka Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar.

Kakakin Rundunar, SP Gambo Isah, ya ce, “Sun tafi da mutum 40, amma Allah cikin ikonSa lokacin da muka samu labari, ba tare da bata lokaci ba, jami’an tsaron suka bi sawun maharan kuma an yi nasarar ceto mutum 30 a lokacin.”

Sai dai ya ce akwai mutum 10 da ba a san inda suke ba, amma babu tabbacin ko suna hannun ’yan bindigar.

“Da safiyar yau, mun je don tantancewa a inda muka samu cewar mutum 10 ne a yanzu ba a san inda suke ba kuma muna ci gaba da bincike”, a cewar SP Gambo.

Masallacin da aka sace mutum 40 a unguwar Kwata (Abatuwa) da ke Jibiya.

Yadda aka sace masu sallar Tahajjud 

’Yan bindiga dauke da muggan makamai sun kutsa masallacin ne da tsakar dare, suka yi awon gaba da mutum 40 daga cikin masu sallar Tahajjud kafin wayewar garin Litinin.

Da yake bayyana yadda abin ya faru, SP Gambo Isah, ya ce ’yan bindigar, “sun yi harbe-harbe a sama kuma sun saci masallata wadanda suka fito domin yin sallar Tahajjud.”

Maharan sun yi wa masallacin dirar mikiya ne da misalin karfe biyu na dare, inda da farko suka yi awon ga da masallata 47, amma bakwai daga ciki suka tsere daga hannunsu.

A kan haka ne daruruwan matasa da ’yan sa-kai suka yi shiri da jihan maharan a hanyar shiga garin ta Daddara, Kukar Babangida da Magama.

Sai dai ya ce sun yi rashin sa’a saboda maharan sun sauya hanya suka biyo ta kusa da Asibitin Yunusa Dantauri.

Ya kara da cewa, ’yan bindiga ba su yi harbi ko sau daya ba har sai da suka gama tattare masallatan suka kama gabansu.

SP Gambo ya ce, “Sabon masallaci yana nan a kan hanyar zuwa Madatsar ruwa ta Jibiya, inda akwai karancin zirga zirgar mutane wanda hakan ne ya bai wa ’yan bindigar damar kawo wannan hari.”