✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka ci zarafin jami’in diflomasiyyar Najeriyar A Indonesiya

Indonesiya ta nemi afuwar gwamnatin Najeriya kan wulakanta mata jami'in diflomsiyya.

Jami’an shige da fice na kasar Indonesiya sun ci zarafin wani jami’in diflomasiyyar Najeriya a Jakarta, babban birnin kasarsu.

Lamarin y faru ne a gaban Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Indonesiya a ranar Asabar, ko da yake kawo yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin lamarin ba.

Ganin munin abin da ya faru, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyema, ya gayyaci Jakadan Indonesiya a Najeriya, Usra Hendra Harahap zuwa ofishinsa.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce wakilin na Indonesiya ya tabbatar da cewa lamarin ya faru a kasarsa kuma ya nemi afuwa.

“Kafin a gayyaci Jakadan, Gwamnatin Najeriya ta aike da takardar nuna bacin ranta a hukumance ga Gwamnatin Indonesiya.

“Gwamnatin Indonesiya ta nemi afuwar Najeriya kan yadda jami’an shige da ficenta suka tsare jami’in ofishin jakadancin Najeriya, a Jakarta babban birnin kasarsu.

“Jakadan ya yi bayanin abin da ya fahimci cewa shi ne ya jawo matsalar kuma ya nemi gafara ba tare da bata lokaci ba a madadin Gwamnatin Indonesiya.

“Ya tabbatar da cewa tuni jami’an shige da fice da suka aikata laifin suka je Ofishin Jakadancin Najeriya don neman afuwar Jakadan da kuma jami’in diflomasiyyar da suka suka ci zarafinsa.”

Da take bayyana fushinta kan abin da ya faru, Ma’aikatar ta ce, “Abin da ba za a lamunta ba ne” domin ya saba wa dokar kasa da kasa da kuma Yarjejeniyar Vienna ta huldar diflomasiyya da jakadanci tsakanin kasashen duniya.

A wani bidiyon da yake yawo a kafafen sada zumunta, an ga wasu mutane uku fararen fata suna kokawa da wani bakar fata a cikin mota sun shake shi.

Mutumin da ake wuyansa a kan kujerar motar yana ta neman dauki yana cewa yan ihu yana cewa “Wuyana… ba na iya numfashi!” Su kuma mutanen na ci gaba da shake shi.