✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka dawo gasar Bundesliga ba tare da ‘yan kallo ba

A ranar Asabar ne kungiyoyin kwallon kafa a kasar Jamus suka dawo gasar Bundesliga bayan da suka kwashe tsawon makonni cikin kulle a dalilin cutar…

A ranar Asabar ne kungiyoyin kwallon kafa a kasar Jamus suka dawo gasar Bundesliga bayan da suka kwashe tsawon makonni cikin kulle a dalilin cutar coronavirus.

Dawowar da gasar tayi dai, yazo cikin tsauraran matakan kariya daga yaduwar cutar wadanda suka hada da: bada tazara tsakanin ‘yan wasa masu jiran canji, kyallen rufe fuska da kuma kwallaye da aka fesa musu maganunguna.

Gasar ta Bundesliga ta zamo babbar gasa ta farko da ta dawo wasanni duk da halin da ake ciki na annobar coronavirus inda ake saran ‘yan kallo kusan biliyan daya ne suka kalli wasannnin a kafafan talabijan.

Abin da yasa aka dakatar da wasannin

An dakatar da manyan gasannin biyu na kwallon kafa a kasar tun tsakiyar watan Maris saboda bulla da kuma yaduwar cutar coronavirus a kasar ta Jamus.

A cikin wasanni da aka bude dawowar dai akwai fafatawar da aka yi tsakanin kungiyar Burossia Dortumund da Shalke 04.

Hakan yasa ‘yan kallo da dama da suka yi kewar kwallon kafa suka bude akwatunan talabijan din su saboda kallon wasannin.

Hasashen masu kallon wasannin

Duk da hasashen da shugaban kungiyar Bayern Munich, Karl-Heinz Rummenigge ya yi na cewa za a samu ‘yan kallo kimanin biliyan daya da zasu kalli wasannin amma yanayin yadda aka gudanar da wasannin baizo wa ‘yan kallo da wata burgewa ta azo a gani ba.

Filin wasan kungiyar Dortmund Iduna Park mai daukar kimanin ‘yan kallo dubu 81 ya kasance fayau inda mutane basu fi 300 ba.

Wadannan sun hada da ‘yan wasa, ma’aikatan horarwa, ‘yan jaridu, ma’aikatan tsaro saboda rage yiwuwar yaduwar cutar.

Yanayin shiru a filin wasan yasa duk wani motsin kwallo ya ke bada wani amshi a na’urar daukar sauti da ake amfani dashi a filin.

A cikin wannan yanayi ne aka buga daya daga cikin wasanni masu zafi a gasar tsakanin Dortmund da kungiyar ta Shalke 04.

Hukumomin gasar ta Bundesliga dai sun matsu a kammala gasar ne kamin karshen watan Yuni saboda kaucewa fadawa cikin rikice-rikicen kwantiragin ‘yan wasa.

A gefe guda kuma, sai da hukumomi suka girki ‘yan sanda a wajen filin wasannin saboda hana ‘yan kallo taruwa.

“Karon batta irin wannan ba tare da ‘yan kallo ba wani sabon kalu bale ne garemu” Inji wani dan sanda a Dortumund din lokacin da yake kira ga ‘yan kallo da su zauna a gidajen su.

Hukumomin gasar sun bada damar canji sau biyar saboda rashin samun damar yin atisaye da kuma yadda za a buga wasanni ba tare da kakkautawa ba.

Sakamakonnin wasanni shida da aka buga ranar Asabar dai sun tashi kamar haka;
____________________________________________________________________
Augsburg 1-2 Wolfsburg

Fortuna Dusseldorf 0-0 Paderborn

Hoffenheim 0-3 Hertha Berlin

RB Leipzig 1-1 Freiburg

Borussia Dortmund 4-0 Schalke 04

Eintracht Frankfurt 1-3 Borussia Moenchengladbach