✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe mutum 45 a rikicin manoma da makiya ya Nasarawa

Mutum 5,000 sun yi kaura a yayin da ’yan sanda ke zargin harin ramuwar gayya a kananan hukumomi uku

Mutum 45 sun rasu, wasu 5,000 kuma sun yi kaura a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a Kananna hukumomin Lafia, Obi da Awe a Jihar Nasarawa.

An jikkata wasu mutum 27 a shi wannan rikicin shugabannin manoma da makiyaya, wanda ya samo asali bayan hare-hare da aka fara kaiwa ranar Juma’a da safe, aka yi ta dauki-ba-dadi har zuwa ranar Lahadi da dare.

Majiyar Aminiya ta ce akalla manoma 5,000 ne rikicin ya tilasta wa yin kaura daga gidajensu a wasu kauyuka 12 da ke kananan hukumomin uku, inda wadanda aka jikkata ke samun kulawa wa asibitoci daban-daban.

‘Daukar fansa ne’

Ganau sun shaida wa wakilanmu cewa an dauki kwanaki ana rikicin a al’ummomin na manoma da makiyaya.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Nasarwa, ASP Ramhan Nansel, ya ce tun ranar Juma’a aka kai musu karar cewa wani mutum a kauyen Gidan Washi a Karamar Hukumar Obi ya kai wa wasu mutane masu dauke da makamai hari ya kashe su.

Daga nan Kwamishinan Rundunar, Adesina Soyemi, ya sa Babban Baturen ’Yan Sandan Karamar Hukumar Obi ya je ya gane wa idansa abin da ke faruwa, shi kuma ya je suka dauke gawar aka kai ta asisbiti domin gudanar da bincike, kafin daga baya aka ba wa iyalan mamacin domin yi mata jana’iza bisa tsarin Musulunci. 

Ya ce: “Ana cikin gudanar da bincike ne wasu mutane daga kauyen Hangara a Karamar Hukumar Lafia suka kai harin da ake zargin na ramuwar gayya ne a kauyen Kwayero da ke Karamar Hukumar Obi.

“Sun kashe Sani Dauda, Danjuma Liambee, Uloho Jerry, Shedrack Kente, Boniface John, Tersoo Clement, Gwanje Soja and Ayuba Ali; ’yan sanda sun gano gawarwakin kuma sun kai su asibiti.

“An tura rundunar hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji yankunan domin tabbatar da doka da oda da kuma cafko wadanda suka yi wannan danyen aiki,” a cewarsa.

Ko a watan jiya, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki kauyen Ashige a Karamar Hukumar Lafiya suka bindige Fulani makiyaya biyu, lamarin da ya haifar da tarzoma, kafin daga bisani jami’an tsaro su shawo kan jama’ar yankin.

Da yake jawabi a kan lamarin, Shugaban Kungiyar Al’ummar Tibi a Jihar Nasarawa (TID), Mista Peter Ahemba, ya ce an gano gawarwakin mutum 12 ’yan kabilarsa a kauyukan da abin ya faru a kananan hukumomin uku.

Mutanen su hada da Chabo, Daar, Tse-Udugh, Ayaakeke, Kyor-Chiha, Usual, Hagher, Joor, Angwan, Ayaba, Tyungu da kuma Ugba.

“An tarwatsa mutum sama da 5,000 daga gidajensu, yanzu sun samu matsuguni a garuruwan Obi da Agwatashi, wadansu kuma sun koma da zama a wurin ’yan uwansu a Karamar Hukumar Lafia.”

“Wasu da dama ba a gan su ba tun da suka shiga daji, babu tabbacin ko har yanzu suna raye,” inji shi, yana mai cewa “Babu abin da al’ummar Tibi suka yi da za a kai musu hari.”

Don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar ta da tarayya da su tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin tabbatar da zaman lumana.

Da yake jawabi, Gwamnan Jihar Nasarwa, Abdullahi Sule, ya ce gwamnatinsa ta fara farautar maharan da suka kashe Fulani makiyaya da manoma ’yan kabilar Tibi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin zaman kwamitin tsaron jihar wanda hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da shugabannin kabilun biyu suka halarta.

Ya shaida musu cewa gwamantin ba za ta zura ido wasu bata-gari na salwantar da rayukan mutanen da ta tsaya kai da fata domin karewa ba.

Ya shaida musu cewa ya kira zaman ne domin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa a Obi, Awe da kuma Lafia.

A cewarsa, “Ana kashe mutane haka kawai, wanda bin Allah wadai ne kuma gwamnatinmu ba za ta lamunta ba.”

Gwamnan ya shawarci al’ummomin jihar da su zauna lafiya da junansu, sannan ya yi wa shugabanninsu kashedi cewa su rika yi wa harshensu linzami domin guje wa kalaman da ke iya harzuwa jama’a su tayar da fitina.

“Za a tura kayan tallafi ga mutanen da suka yi kaura sannan gwamnati za ta tattauna da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da mutane sun koma gidajensu su ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda suka saba,” a cewarsa.

’Yan Kaduna na kaura bayan ’yan bindiga sun kashe basarake

Hakan nan zuwa ne bayan ’yan bindiga sun kashe Magajin Garin Idasu a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, Malam Magaji Ibrahim, a ranar Lahadi.

An yi masa kisan gilla ne washegarin da ’yan bindiga suka kashe mutum 40 a wasu kananan hukumomin jihar, ciki har da Giwa.

Wani shugaban matasa a kauyen Rahiya, Ridwan Abdulhadi, ya ce harin ya sa kusan kashi 70 cikin 100 na mutanen Idasu sun yi kaura domin samun tsira a Karamar Hukumar Zariya da garin Giwa.

Wani mazaunin garin, Sharehu Idasu, ya ce ’yan bindigar sun kashe basaraken ne bayan ya fito daga gidansa yana neman a kawo musu dauki bayan ’yan bindigar sun kai wa garin hari a cikin dare kafin wayewar garin Litinin.

Tuni dai aka yi jana’izar dattijon bisa tsarin addinin Islama.

Maharan da suka far wa garin a kan babura sun kai harin ne bayan wani makamancinsa da ’yan bindiga suka kai a kauyen Rahiya ta karamar hukumar a ranar Asabar da yamma.

“Kashi 70 cikin 100 na mutane sun yi kaura zuwa Giwa da Zariya tare da iyalansu saboda abin da ya faru…mutum 23 aka kashe a Rahiya kadai, 21 daga cikinsu magidanta ne, biyu ne kawai marasa aure,” inji wani mazaunin garin. 

Ya kara da cewa wasu mutum hudu kuma sun samu raunuka, sannan marayun da aka bari na bukatar tallafi cikin gaggawa.

A ranar Litinin mun kawo rahoton yadda mahara suka far wa kauyukan Kauran Fawa, Marke da Rahiya da ke mazabar Idasu a Karamar Hukumar Giwa jhari.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya sanar a ranar Lahadi cewa mutum 38 ne aka kashe a kauyuka ukun.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, bai samu ba, a lokacin da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa game da kisan basaraken da aka yi.

 Daga Sagir Kano Saleh, Umar Muhammed (Lafia), Lami Sadiq (Kaduna) da Dickson Adama (Jos)