✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe mutum 8 a kwanton baunan da aka yi wa Sarkin Kauran Namoda

Mutum takwas ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin Sarkin Kauran Namoda, Manjo Sanusi…

Mutum takwas ne suka rasa rayukansu a ranar Alhamis yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari kan ayarin motocin Sarkin Kauran Namoda, Manjo Sanusi Muhammad Asha mai ritaya a Mararrabar Maska da ke kan hanyar Funtua zuwa Zariya.

Aminiya ta ruwaito cewa a yayin da Sarkin da iyalansa suka tsallake rijiya da baya, mutum takwas daga cikin ayarin da take tafe tare da shi sun rasa rayukansu ciki har da jami’an ’yan sanda uku, dogarawa da wani dan uwansa guda daya.

Titin Zariya zuwa Funtuwa mai nisan kilomita 70 ya yi kaurin suna a matsayin cibiyar da ’yan ta’adda musamman masu fashi da makami ke cin karensu babu babbaka idan hasken rana ya disashe.

Kawun Sarkin, mai rike da sarautar Danjekan Kauran Namoda, Alhaji Abdulkarim Ahmed Asha, ya shaida wa Aminiya cewa da misalin ukun dare suka samu labarin cewa mahara sun yi wa ayarin Sarkin kwanton bauna, lamarin da ya kai ga mutum takwas sun halaka ciki har da wani direba guda.

Mazauna yankin Mararrabar Maska sun labarta wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 8.30 na Yammacin ranar Alhamis kuma da misalin karfe ukun dare suka rika jin sautin harbe-harben bindiga yana tashi na wani lokaci takaitacce.

Binciken Aminiya ya gano cewa ’yan bindigar sun bude wuta ne a kan ayarin motocin, lamarin da ya sanya direban motar da ya dauko dakon Sarkin ya yi gaggawar juya wa, inda ita kuma motar da dauko wani Kawun Sarkin mai rike da rawanin Dan Amaran Kauran Namoda da sauran fasinjojin cikinta ciki har da jami’an ’yan sanda uku da direban ba su tsira ba.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa mutanen motar da ta dauko Dan Amaran Kauran Namoda duk sun fice daga cikinta, inda gabanin su yi wata kyakkyawar tika maharan suka kar su a dokar daji.

Abubakar Ishaq, wani dan uwan daya daga ’yan sandan da aka kashe, ya ce sun ziyarci Babban Asibitin Funtua da ke jihar Katsina domin tabbatar da gawar dan uwansu, inda kuma a nan suka riski gawarwakin wasu mutum bakwai da aka killace ciki har da dogarawan Sarki da ta wani mai rike da kambun sarauta.

Abubakar ya kara da cewa an garzaya da gawawarkin wadanda suka mutu zuwa birnin Gusau na jihar Zamfara, inda a nan aka nufaci yi masu sallar jana’iza.

Daga bisani kuma an sake garzaya wa da gawawwakin zuwa garin Kauran Namoda inda babban limamin masallacin Juma’ar garin ya jagoranci sallar jana’iza wadda dubban mutane suka halarta ciki har da Sarki Gusau.