✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe Tolulope, inji sojoji

Motar ta buge ta, ta fadi kasa kanta ya bugi kasa motar ta take ta.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya fitar da sunayen wadanda ake zargi da kashe mace ta farko mai tuka jirgin sama na yaki a kasar, Tolulope Arotile.

Daraktan yada labarai na rundunar, Ibikunle Daramola ne ya sanar da haka ga manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuli.

Daramola ya ce abokan karatun marigayiyar na makarantar sakandare ne su biyu wadanda dukkanninsu farar hula ne suka kade ta da mota.

“Sun shigo barikin ne domin kai wa matar wani hafsan soji ziyara.

“Suna tafe sai suka hangi marigayiyar, Arotile Tolulope abokiyar karatunsu a sakandare.

“Ko da suka wuce ta, sai wanda ke tuka motar ya yiwo baya da motar cikin hanzari da zummar ya riske ta, a lokacin da ta ke tafe ta bayansu, a haka ne motar ta buge ta, ta fadi kasa kanta ya bugi kasa motar ta take ta.

“Nan take aka kai ta Asibitin Sojin Sama da ke barikin inda aka tabbatar ta mutu da misalin karfe 04;45 na yamma.

“An kuma tsare abokan nata inda aka yi masu gwaji aka tabbatar ba su sha kayan maye ba, an kuma gano wanda ke tuka motar, ba shi da lasisin tuki”, inji shi.

Ibikunle Daramola yace, kasancewar lamari ne da ya shafi farar hula, rundunar sojin saman za ta mika su ga rundunar ‘yan sanda wacce za ta ci gaba da bincike ta kuma gurfanar da su a kotu.