✕ CLOSE Kiwon LafiyaRa’ayoyiRa'ayin AminiyaRahotoAminiyar KurmiHotunaGirke-GirkeSana'o'iKimiyya da Kere-Kere

Yadda aka sace kananan yara 39 a gona a Katsina

Ana tsaka da aiki a gona ’yan bindiga suka bude wa ma'aikata wuta suka tafi da yara 39

Iyaye a kauyen Mairuwa a Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina sun shiga tashin hankali bayan ’yan bindiga su yi garkuwa da ’ya’yansu 39 da ke tsaka da aiki a gona.

Al’umnar kauyen sun roki gwamnati ta kai musu dauki bayan ’yan bindiga sun ritsa masu aikatau a wata gona, ciki har da kananan yara mata da maza, suka tisa keyar 39 daga cikinsu.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa wakilinmu cewa a harin na ranar Lahadi, “A kauyenmu na Mairuwa kadai kananan yara 33 aka tafi da su, cikinsu har da ’yan mata da ake shirin yi wa aure.”

Mazauna kauyen Mairuwa sun ce ’yan bindiga sun ritsa masu aikin ne gonar suka yi ta harbe-harbe, kafin su tasa keyar yaran.

Majiyarmu a kauyen ta ce yawancin manyan da ke gonar a lokacin harin sun samu sun tsere.

Wani mazaunin kauyen ya ce wakilan mai gonar sun kai ma’aikata gonar ne bayan mai gonar ya biya ’yan bindiga Naira miliyan daya.

Majiyarmu ta ce ’yan bindiga, “Sun nemi mai gonar ya ba su Naira miliyan uku kafin ya girbe abin da ya noma, kuma ya ba su kafin alkalami miliyan daya, ya yanke shawarar ci gaba da aiki kafin ya ba su cikon, amma abin takaici sai suka ki amincewa.”

Shi ma wani dan garin, ya ce, “Mai gonar a Huntuwa yake, wakilinsa ne dan nan garin.

“’Yan bindigar sun kira mu a waya suna neman kudin fansa Naira miliyan 30.

“Sun ce sun je gonar ne domin su dauke mai gonar ko wakilinsa, amma da suka je ba su sami kodaya daga cikinsu ba, shi ne suka ce bari su tafi da ma’aikatansu.”

Aminiya ta gano cewa iyayen yaran da aka sace sun yi dafifi a gidan wakilin mai gonar a ranar Litinin, suna zargin sa da jefa rayuwar ’ya’yansu cikin hadari.

Daga bisani dai ’yan sanda sun shiga tsakani, suka tsare shi, kafin daga baya su sako shi.

Rahotanni sun nuna cewa mazuna yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Jihar Katsina na cikin damuwa saboda yadda ’yan bindiga ke tilasta musu biyan makudan kudade kafin su girbe amfanin gonarsu.

Wani mazaunin kauyen Katoge da ke Karamar Hukumar Kankara ta jihar ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan bindiga sun sanya wa mutanen kauyen harajin Naira miliyan biyu kafin su bari su girbe abin da suka noma, amma daga baya suka rage kudin zuwa Naira dubu 600.