✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka sace kanina tsohon Hadimin Gwamna a masallaci —Lawal Maikifi

Wata uku da sace Alhaji Uba Boris, amma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.

Sace wani fitaccen matashin dan siyasa dan jam’iyyar APC, Alhaji Uba Boris, a cikin garin Bauchi fadar Jihar Bauchi ya fara sanya tsoro da firgici a zukatan jama’ar jihar, musamman ’yan siyasa saboda ganin yau sama da wata uku ke nan da sace shi, ba tare da an tutubi iyalansa don neman kudin fansa ba kamar yadda aka san masu garkuwa da mutane suna yi.

Wannan ya sa mutane da dama a jihar suke alakanta sace shi da siyasa, kuma hakan ne yake sanya tsoro a zukatan jama’a, ganin cewa ana tunkarar zaben 2023.

Fasalin yadda aka sace Alhaji Uba Boris wanda matashi ne da yake girgiza siyasar jihar ya sa mutane suka fi alakanta sace shi da siyasa, musamman ganin an sace shi ne kwanakin kadan da ya fara jagorantar kiran tsohon Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Siddique Abubakar ya fito takarar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar APC.

Bayanai sun ce an sace matashin dan siyasar ne kwanaki kadan bayan ya fara ganawa da mata da matasa kan wannan yunkuri.

Tun lokacin da aka sace shi wadansu mutane a birnin suke ganin sace shi yana da nasaba da siyasa yayin da wadansu suke ganin makiya ne suka sace shi, wadansu kuma suna zargin jami’an tsaro ne da sace shi.

Sai dai yanayin yadda aka sace shi a kan manyan baburan nan na zamani, ya jefa shakku a kan zargin jami’an tsaro duk da cewa mutanen da suka sace shi, sun je masallacin ne da kayan jami’an tsaron.

Yayan Uba Boris, Alhaji Lawal Maikifi, ya shaida wa Aminiya cewa fiye da wata uku da aka sace kanen nasa a daidai lokacin da yake cikin Sallah a wani masallaci, har zuwa yanzu babu labarinsa.

Alhaji Lawal ya ce bayanai sun nuna cewa wadanda suka sace sun shiga cikin masallacin ne sanye da kaya irin na jami’an tsaro a jikinsu.

Kuma iyalai da abokan kanen nasu sun bincika dukkan wuraren jami’an tsaro amma dukkansu sun ce ba su suka sace shi ba, kuma ba su da masaniya kan ko an turo wadansu ne daga wani ofishinsu su kama shi.

Alhaji Lawal Maikifi ya ce “Kanena yana Sallah a masallacin wajen sayar da motoci na A.A. Naira aka zo aka sace shi a daidai lokacin da ya yi ruku’u zai mike.

“Haka aka tafi da shi, kuma tunda aka tafi da shi ba mu ji komai daga gare shi ba, yanzu dai muna mika kukanmu ga Allah amma ba ma zargin wani da sace shi.”

Ya kara da cewa, “Lokacin da aka sace shi da mutane a cikin masallacin, cikin ikon Allah wadansu suna alwala ba su samu shiga cikin masallacin ba wadansu kuma da suka ji hayaniya haka suka yanke Sallar, suka fito.

“To ka san mutumin da ya zo da bindigogi saboda tsoron abin da ka iya biyowa baya, sai mutanen suka hakura har aka tafi da shi, yau fiye da wata uku.”

Ya gode wa ’yan sanda da ’yan sandan farin kaya wadanda ya ce a kullum suna kokari kwarai da gaske domin ganin sun samo labarinsa su ceto shi.

Ya ce a kullum Kwamishinan ’Yan sandan Jihar yana karfafa musu gwiwa cewa suna tsaye sosai domin ganin an gano shi kuma in sun samu labarin inda yake za su sanar da iyalansa.

Alhaji Lawal Maikifi ya kuma gode wa jama’a da sauran masoyansu da suke taya su da addu’o’in Allah Ya bayyanar da shi.

Ya ce iyalan kanen nasa sun shiga cikin wani mawuyacin hali musamman matansa biyu da ’ya’yansa 17. Ya ce matarsa daya ma jininta ya hau ta kwanta a asibiti na mako daya yanzu kuma tana kwance a gida babu lafiya.

Alhaji Uba Boris ya taba rike mukamin Mai Tallafa wa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, kan Harkokin Matasa, daga bisani ya zama Darakta Janar na Cibiyar Horar da Sana’o’i ta Malam Isa Yuguda inda ya horar da daruruwan matasa sana’o’in dogaro da kansu.

Binciken da wakilin Aminiya ya yi, ya gano cewa kafin a sace shi daya daga cikin shugabannin mata na Jam’iyyar APC ta kira shi wani taro a rukunin gidajen da ake kira Gida Dubu, inda ya yi kamar ba zai je ba, amma suka matsa masa ya je, saboda a ganinsa ba a fara harkokin siyasa ba.

A kan hanyarsa ta zuwa taron wadansu mutane a cikin wata mota mai bakin gilashi sun yi yunkurin sace shi amma Allah Ya kare shi, sai dai mako biyu bayan haka ne aka sace shi.

Shi da iyalansa dai ba sa zargin shugabar matan da kullla wani makirci ko sa hannu wajen sace shi.

’Yan uwa da makwabta da wakilinmu ya tuntuba, sun bayyana Alhaji Uba Boris a matsayin mutumin kirki mai taimako mai kuma kokarin yin tarbiyyar kirki ga iyalansa, inda suka yi jimamin rashinsa tare da addu’ar Allah Ya bayyana shi.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Alhaji Uba Ahmed Nana ya ce jam’iyyar tana yin duk abin da za ta iya don ganin an gano inda Uba Boris yake.

Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Bauchi, Mista Sylvester Abiodun Alabi ko Kakakin Rundunar ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Amma wani babban jami’in ’yan sanda ya shaida wa wakilinmu cewa an riga an fara bincike a ciki da wajen jihar, kuma kullum ana bibiyar lamarin, da zarar an samu labarin wurin da aka boye shi in Allah Ya so ’yan sanda za su je su karbo shi.

A watannin baya Aminiya ta bayar da rahoton sace Ko’odinetan Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Abdulkadir a Karamar Hukumar Ningi, wato Alhaji Mato Burra wanda shi ma har yanzu babu labarinsa.

Alhaji Mato Burra mai shekara 67 an sace shi ne a gonarsa da ke garin Burra tun cikin watan Fabrairun bana, kimanin wata takwas ke nan, amma har yanzu babu labarinsa.

Sace Alhaji Mato Burra wanda ke rike da sarautar Kauran Burra ta jefa tsoro da fargaba a zukatan al’ummar yankin.

Iyalansa sun ce ana zargin an kai shi Jihar Zamfara ne, kuma an yi nema har a dazuzzukan jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara amma Allah bai sa an same shi ba.

Sun ce masu garkuwa da mutanen sun taba kira suna neman a kai musu Naira miliyan biyar a wani daji a Jihar Katsina, bayan an kai kudin wadanda suka kai kudin ma sai da aka fanshe su shi kuma babu wani labari a kansa.

Sun ce rashin tuntuba daga masu garkuwar da kuma jami’an tsaro ya kara musu damuwa domin Alhaji Mato Burra yana fama da hawan jini, kuma ba ya tare da magani lokacin da aka sace shi, wanda hakan yake sanya musu damuwa kan ko yana raye ko ba ya raye.

Sun roki Rundunar ’Yan sandan Jihar da Gwamnan Jihar Bauchi su kara kokari domin ganin an samu bayanin halin da yake ciki.

Kakakin Jam’iyyar PDP na Jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari ya ce jam’iyyar ta yi Allah wadai da sace wannan dattijon danta da aka yi. Ya ce jam’iyyar tana iyakacin kokarinta don ganin an kubutar da Alhaji Mato Burra.

Shugaban Karamar Hukumar Ningi, Alhaji Mamuda Hasan Tabla wanda mataimakinsa da ne ga Alhaji Mato Burra, ya shaida wa Aminiya cewa har yanzu babu wani bayani da suka samu a kan inda aka kai Alhaji Mato Burra. Ya ce wadanda suka sace shi ba sa magana, lamarin da ya ce ya jefa mutanensu a cikin rudani.