✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka sace motar N54m cikin minti 1

Wanda bai ba taga gabin irin makullin motar ba, ya sace ta a cikin dakika 63

Barayi sun saci jiki zuwa cikin wani gida, inda cikin minti daya suka sace motar alfarma wadda kudinta ya kai Niara miliyan 54.4.

Ma’auratan da aka sace wa motar, kirar Range Rover, sun bayyana cewa bidiyon da kyamarar tsaro ta CCTV da ke gidansu ta dauka, ya nuna yadda barayin suka shida cikin gidan suka sace motar a cikin dakika 63 kacal.

“Idan ka kalla a CCTV, za ga abin mamaki, mutumin da bai ba taga gabin irin makullin motar alfarmar ba, ya yi awon gaba da ita a cikin dakika 63 kacal,” in ji magidancin mai suna Mista Anthony Wilson da ke yankin Essex na kasar Birtaniya.

Bayan wata guda, jami’an tsaron kasar suka gano motar a tashar jiragen ruwa ta Tilbury an loda ta a cikin kwantaina zuwa kasar Jamhuriar Dimokuradiyyar Kwango.

A lokacin da motar ta yi batan dabo, ma’auratan sun shaida wa jami’an tsaro cewa sun wayi gari ne kawai suka ga babu motar, ba su ma ankara cewa barayi sun shiga gidan a cikin dare ba.

Da take siffanta yadda aka dauke motar a watan Yulin 2022, matarsa mai suna Danielle ta shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa ’yan sanda sun yi zargin barayin sun biyo sawunta ne zuwa gidan.

Karuwar satar motoci a Birtaniya

’Yan sandan yankin Essex sun ce an samu karuwar sace-sacen motoci a Birtaniya, musamman bayan bullar COVID-19 da kuma tsadar rayuwa.

Sun bayyana cewa a shekarar 2021 an kwato motoci 480 daga  hannun barayi, a 2022 kuma aka kwato motoci 600.

Babban Jami’in Dan Sanda Mai Bincike Kan Satar Motoci a Birtaniya, Renato Schipani, ya ce, akasarin motocin da ake sacewa a kasar ana kai su kasashen Afirka irin su Kenya, Uganda da Sudan inda amfani da motoci masu kujerar direba a hannun dama.

Renato Schipani, wanda ke aiki da Hukumar ’Yan Sanda ta Kasa da kasa (INTERPOL), ya ce yawancin motocin da ake sacewa a Birtaniya kirar SUV na alfarma ne, kamar dai Range Rover da aka dauke wa ma’auratan.

Ya bayyana cewa yawacin kananan motoci da ake sacewa a Kudanci Amurka da Yammacin Turai kuma, barayin na safarar su ne zuwa Yammacin Afirka, kasashen da suka fi amfani da motoci masu kujerar dirabe a hannun hagu.