✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka sace mutum 46 a Katsina

’Yan bindiga sun bukaci a biya su kudin fansa da sabbin takardun Naira bayan sun sace mutum 46 a Jihar Katsina

’Yan bindiga sun nemi a biya su kudin fansa da sabbin takardun Naira bayan sun yi garkuwa da mutum 46 a wasu hare-hare biyu a kauyukan kananan hukumomin Funtua da Batsari na Jihar Katsina.

Mahara kusan 40 a kan babura, sun kashe mutum daya, suka sace wasu 28, ciki har da  mata da kananan yara a safiyar ranar Juma’a, a kauyen Karare da ke Karamar Hukumar Batsari.

“Daga cikin mutum 28 da suka sace har da wasu dalibai,” in ji wani ganau da ya ce maharan sun kashe mutum daya a yayin da suka shiga garin suna harbi kan mai uwa da wabi.

Rahotanni sun nuna daga cikin yaran da aka yi garkuwa da su har da dalibai daga kauyen Kokiya da ke hanyarsu ta zuwa Makarantar Sakandaren Je-ka-ka-dawo ta Gwamnati a kauyen Karare.

Shaidan ya ce, “Daga baya maharan sun sako hudu, wato Malam Ladan da ’ya’yansa uku.”

Kudin fansa da sabbin takardun Naira

“Sun kuma turo da sako cewa ba za su karbi tsoffin takardun kudi ba a matsayin kudin fansa.

“Daga baya mutum daya ya tsere daga hannunsu, saboda haka yanzu mutum 23 na hannun ’yan bindiga, amma masu garkuwar ba su nemi kudin fansa ba tukuna.”

Shi ma wani mazaunin garin da ya tabbatar da kisan, ya bayyana cewa yana asibiti lokacin da aka kai harin, amma ya tsallaka katanga ya tsere.

An sace mutum 18 suna cikin sallah a masallaci

A daya harin kuma, ’yan bindiga sun far wa wani masallaci a kauyen Maigamji da ke kan Babbar Hanyar Funtua zuwa Dandume, suka bude wuta kan mutanen da ke tsaka da Sallar Isha’a.

Tsohon Kansilan Gundumar Dangamji, Lawal Maigamji, ya ce, maharan sun harbi limamin da ke jan sallar da wani mutum daya, sannan suka sace mutum 18 daga masallacin a harin na ranar Asabar.

Lawal Maigamji, ya ce, “Yan bindigar sun yi wa masallacin zobe a yayin da ake jam’in Sallar Isha, suka harbi Imam Yusha’u da Hussaini Jamo, sannan suka yi awon gaba da mutum 18 zuwa cikin daji.”

Ya ce, a halin yanzu mutanen biyu suna samun kulawa a Babban Asibitin Funtua, sannan an yi sa’a mutum hudu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a masallacin sun tsere kafin ’yan bindigar su isa da su maboyarsu.

Mun ceto mutum hudu —’Yan sanda

Ko da muka nemi karin bayani daga mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isa, kan harin kuayen Karare, ya shaida mana cewa rundunar na gudanar da bincike domin tabbatar da adadin mutanen da abin ya rutsa da su.

Ya ce, “Mun samu rahoto, amma yawan mutanen da aka bayan sun bambanta, wasu sun ce mutum 30 aka sace wasu kuma sun ce bai kai haka ba.

“Saboda haka muna gudanar da bincike domin tantance gaskiyar sannan an riga an fara aiki domin kubutar da mutanen wadannan ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

“A harin Yargamci, mutum 13 sun bace, biyu sun samu raunin harbi, ciki har da limamin da ke jan sallar, sannan an kubutar da mutum hudu.

“Jami’anmu na aiki tare da ’yan banga domin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su,” in ji shi.

Daga: Sagir Kano Saleh, Mahmoud Idris & Tijjani Ibrahim (Katsina)