✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka tsaurara tsaro a Majalisa kafin mika kasafin 2022

Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a zauran Majalisar Tarayya.

An tsaurara matakan tsaro a harabar Majalisar Tarayya gabanin gabatar da daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari zai yi a ranar Alhamis.

Jami’an tsaro sun yi wa harabar Majalisar tsinke, inda suke tsaurara bincike a kan duk wanda da zai shiga ko ya fita daga harabar.

Wakilinmu ya lura cewa jami’an tsaron ba sa barin duk wanda ba shi da alamar izinin shiga wurin ya wuce.

Tun a ranar Laraba Buhari ya sanar da zaurukan majalisar – Majalisar Dattawa da ta Wakilai – cewa yana so ya gabatar musu da kasafin da misalin karfe 12 na ranar Alhamis.

Kasafin na 2022 an ware masa Naira tiriliyan 16.39, wanda ya karu da sama da Naira tiriliyan 2.7 na kasain 2021 na Naira tirliyan 13.6.