✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi add’uar tunawa da tsohon Shugaba Yar’Adua

An yi addu’o’i ga tsohon Shugaban Kasa Umaru Yar’Adua bayan shekara 11 da rasuwarsa.

An gudanar da addu’o’i na musamman ga tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa Yar’Adua bayan cikarsa shekara 11 da rasuwa.

Addu’o’in sun gudana ne a garin Katsina a yammacin ranar Laraba, 5 ga watan Mayu, ranar da marigayin ya ciki shekara 11 da komawa ga Mahaliccinsa.

A yayin taron, an yi addu’o’i na musamman gami da karatun Alkur’ani wanda da Malam Usman Mohammed ya jagoranta domin nema wa mamacin gafarar da kuma neman samun zaman lafiya a Najeriya.

Wani sashe na mahalarta addu’ar cika shekara 11 da rasuwar Shugaba Yar’Adua. (Hoto: Ahmed Kabir S/Kuka).

Saukar Alkur’anin wanda aka yi a masallacin Sakatariyar Jam’iyar da ke Katsina ya samu halartar kusoshin jam’iyar na jiha karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri.

Majigiri ya ce ambato wasu daga cikin ayyukan da marigayi Umaru Yar’Adua ya yi a lokacin yana gwamna, da cewa, “Duk wasu ayyukan cigaba da aka samu a Jihar, wannan bawan Allah ne ya yi su ko kuma ya assasa, Gwamna Shema ya karasa ko kuma ake cikin aiwatarwa har a wannan lokacin.

“In za mu ci gaba da bayanin ayyukan marigayin, muna iya kwashe kwana da yini ba mu fadi ko da rabin abin da ya yi ba.

“Kowa ya san irin yadda batun hakar man fetur ya so gagara a kasar nan saboda matsalar ’yan Neje Delta, amma lokacin da ya karbi shugabancin kasar nan, Allah Ya ba shi iko da damar shawo kan matsalar ta hanyar yi masu afuwa bayan yin sulhun da aka samu.

“Yau ga shi yankin Neja Delta ya fi Jihar Katsina zama lafiya da tsaro.

“Ga batun rage farashin litar man da kuma kafa wasu gidajen mai karkashin NNPC wanda hakan ya sa cikin karamin lokaci batun dogon layi a gidajen mai ya zamo labari”, inji Majigiri.

Ya kara tunatarwa tare da jan hankali kan sha’anin tsaro inda ya ce, babu siyasa a ciki, “Domin babu ruwan sha’anin tsaro da dan PDP ko APC ko APGA da sauransu.

“A kan haka, ya zama wajibi a yiwa kasa addu’ar samun zaman lafiya.

“Babu abin da zai ci gaba muddin aka ce babu tsaro a wuri. Saboda haka, wajibinmu ne mu yi wa kasar baki daya addu’a”.