✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi bikin nada Masu Zaben Sarki a Masarautar Karaye

Mahaifin tsohon Gwamna Kano, Rabiu Kwankwaso na cikin Masu Zaben Sarki

Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Ibrahim Abubakar III, ya yi bikin nada masu sarautun nada sarki a Masarautar Karaye da ke Jihar Kano.

A lokacin bikin nadin wanda aka yi a ranar Juma’a a fadarsa da ke garin Karaye, sarkin ya taya wadanda suka samu sarautun murna tare da fatan za su rike sarautun bisa amana.

An dai nada mutane da dama a sarautu daban-daban, wadanda suka hada da mahaifin tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wato Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a matsayin  Makaman Karaye.

Sauran su ne: Alhaji Jibrin Ibrahim Zarewa, Sarkin Ban Karaye

Sanata Bello Hayatu Gwarzo, Sarkin Dawaki Mai Tutan Karaye

Alhaji Mahe Bashir, Dan Iyan Karaye

Alhaji Ibrahim Ahmad, Madakin Karaye.

Sarkin Karaye ya kuma nada ‘Yan Majalisar Sarki da suka hada da Alhaji Sama’ila Gwarzo, tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha kan tsaro, a matsayin Walin Karaye.

Ya kuma nada Alhaji Musa Muhammed a matsayin Wazirin Karaye.

Bayan kammala nade-naden Sarautun, Gwamna Abdullahi Ganduje da Sarkin Karaye sun halarci daurin auren diyar sarkin, Gimbiya Nafisa Ibrahim Abubakar.

Taron ya kuma samu halartar manyan mutane daga cikin masarautar, Jihar Kano, da ma wasu masarautun da suka hada da: Wakilin Sarkin Musulmi Sultan Abubakar III, Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid, wakilan sarkuna Gwandu, Kano, Bichi, Rano, Gaya da kuma Daura da sauran jami’an gwamnatin jihar Kano da dama.