✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano

Dubban mutane ne suka yi dafifi a yammacin ranar Litinin wajen halartar jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano, Hajiya Maryam Ado Bayero wacce Allah Ya yi wa…

Dubban mutane ne suka yi dafifi a yammacin ranar Litinin wajen halartar jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano, Hajiya Maryam Ado Bayero wacce Allah Ya yi wa cikawa a kasar Masar bayan wata rashin lafiya mai gajeren zango.

Shugaban Limaman Kano, Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen ne ya jagoranci sallar jana’izar da aka yi a Kofar Kudu da ke Fadar Masarautar Dabo.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa wanda ya kasance dan uwa ga marigayiyar, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya jagoranci tawagar Gwamnati Tarayya wajen halartar jana’izar da ta hadar da Ministan Tsaro, Bashir Magashi da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

Sauran ’yan tawagar sun hada da Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Ministan Harkokin ’Yan sanda, Maigari Dingyadi, Ministan Ruwa, Suleiman Adamu da kuma Yusuf Buhari, dan Shugaba Muhammadu Buhari.

Kabarin da aka sanya gawar Marigayiya Maryam Bayero
Yayin da ake sanya gawar Marigayiya Maryam Bayero a makwanci
Yadda Mutane suka yi dafifi wajen jana’izar Marigayiya Maryam Bayero

Haka kuma, jana’izar ta samu halarcin wakilai daga wasu manyan masarautu na kasar ciki har da ta Fadar Sarkin Musulmi, Masarautar Ilorin, Hadejia, Katagum, Bauchi, Fika, Kagara, Kanam, Kazaure, Karaye, Rano, Dass, Potiskum, Ningi, Keffi da sauransu.

An binne Mai Babban Dakin ce a Sheka Hubbare, mashimfidar da ke cikin Fadar Masarautar Kano wacce ake saba binne duk wata Sarauniya da ta shude tun daga zamanin Daular Fulani da masarautar ta samo asali.

Hajiyar Maryam Bayero mai shekara 89, wadda aka fi sani da Mama, ko Mama Ode, ta rasu ne a safiyar ranar Asabar da ta gabata a wani asibiti da ke birnin Alkahira na kasar Masar.

Marigayiyar ita ce Mahaifiyar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero kuma mahaifiyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, baya ga kasancewar ta babbar matar Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero kuma ’yar sarki a gidan Sarautar Ilorin da ke jihar Kwara.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya da ta kunshi manyan kusoshin gwamnati wajen iso da gawar marigiyar daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano bayan isowarta daga kasar Masar.