✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar Sarkin Lere

Dubban mutane daga bangarori daban-daban na kasar nan ne suka halarci jana’izar marigayin

An yi jana’izar marigayi  Sarkin Lere da ke Jihar Kaduna kuma tsohon Gwamnan mulkin Soja na Jihar Sakkwato, Birgediya Abubakar Garba Muhammad, Mai ritaya.

Jana’izar dai ta gudana ne da yammacin ranar Asabar a fadarsa da ke garin na Lere.

Marigayin ya rasu ne ranar Asabar bayan wata gajerar jinya a wani asibiti da ke Kaduna yana da shekara 77 a duniya.

Dubban mutane daga bangarori daban-daban na Najeriya ne suka halarci Sallar Jana’izar basaraken, wadda Babban Limamin Lere, Sheikh Aliyu Muhammed Sani ya jagoranta.

Da yake zantawa da wakilinmu kan rasuwar marigayin, Sakataren marigayin kuma Sallaman Lere, Malam Murtala Sale ya bayyana cewa babu abin da za su ce, kan rayuwar da suka yi da marigayin sai dai su yi wa Allah godiya.

Ya ce  shekaru 10 da marigayin ya shafe a kan  karagar mulkin wannan masarauta, sun zauna da shi lafiya.

Ya ce a cikin wadannan shekaru, marigayin ya inganta rayuwar al’ummar Masarautar, yana mai cewa ba za su taba mantawa da shi ba.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar akwai Sarkin Jama’a, Alhaji Isah Muhammad da Sarkin Chawai, Alhaji Yahaya Abdullahi da Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Muhammad Sani.

Sauran manyan bakin su ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Sani Dattijo da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar, Alhaji Jafaru Sani da Daraktan Hukumar Samar da Ruwa ta Jihar Kaduna [RUWASSA], Injiniya Ahmed Mannir da Sanata mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta Arewa, Sanata Sulaiman Abdu Kwari da dai sauransu.