Yadda aka yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Abuja | Aminiya

Yadda aka yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Abuja

    Idowu Isamotu da Sagir Kano Saleh

An gudanar da jana’izar sojojin rundunar da ke tsaron shugaban kasa da ’yan bindiga suka kashe a wani hari a yankin Bwari da ke Abuja.

A ranar Alhamis aka kai sojojin su hudu makwancinsu a Makabartar Sojoji da ke Maitama a Abuja.

Tun da farko sai da aka gudanar addu’o’i a Cocin Sojoji na St. Johns kafin a kai su makabartar.

Sojojin, ciki har da hafsoshi hudu, sun kwanta dama ne bayan harin da ’yan bindiga suka kai musu a lokacin da suke dawowa da sintirin dakile harin da ’yan bindiga ke shirin kaiwa a Makarantar Koyon Aikin Lauywa da ke Bwari, Abuja.

Kafin rasuwarsu, sojojin suna aiki ne a Rundunar 7 Guards Battalion, da ke Barikin Sojoji na Lungi a Maitama da kuma 176 Guards Battalion da ke Gwagwalada.

A jawabansu na ta’aziyya, Kwamandojojin rundunonin, Laftanar Kanar Salim Yusuf Hassan da Laftanar Kanar Joshua Kolawole Adisa, sun bayyana marigayan a matsayin jarumai abin koyi wajne kare kasarsu.