✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izyar shugaban Fulani Sale Bayeri

Bayeri ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos bayan gajeriyar rashin lafiya.

An yi jana’izar fitaccen shugaban Fulani, dan kishin kasa kuma tsohon dan jarida, Alhaji Sale Bayeri.

Sheikh Muhammad Nasir Abdulmuhyi ne ya jagoranci Sallar Jana’izar Alhaji Sale Bayari tare da binne shi da safiyar ranar Juma’a, kamar yadda addnin Musulunci ya tanadar.

Sale Bayeri ya rasu ne a ranar Alhamis da dare a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), bayan gajeriyar rashin lafiya.

Sheikh Muhammad Nasir Abdulmuhyi lokacin da ya jagoranci Sallar Jana’izar Marigayi Alhaji Sale Bayari

Shugaban GAFDAN reshen Jihar Filato, Garba Abdullahi Muhammad ne, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar Bayeri.

Kafin rasuwarsa, Bayari ya kasance Shugaban Kungiyar Gan Allah Fulani (GAFDAN), sannan tsohon Sakataren Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), inda ya yi aiki na kimanin shekara 20.

Sannan ya halarci taruka da dama na ciyar da kasa da talakawa gaba, kazalika, ya kasance mai taimakon rayuwar mutane.