✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi wa Sakkwatawa kisan gilla a Anambra

An yi musu kisan gilla ta hanyar cinna wa gidan da suke wuta idan mutum ya fito daga gidan don ya tsira sai a harbe…

Wasu mahauta hudu ’yan asalin garin Salame da ke Karamar Hukumar Gwadabawa a Jihar Sakkwato aka yi wa kisan gilla ta hanyar cinna wa gidan da suke wuta idan mutum ya fito daga gidan don ya tsira sai a harbe shi.

Lamarin ya auku ne a garin Ihiala da ke Jihar Anambra a ranar Litinin da ta gabata, a cewar Sha’aibu Salame da aka fi sani Yaba, dan uwan daya daga cikin mutum hudun da aka kashe.

Yadda abin ya faru

Ya ce, “Yadda abin ya faru kamar yadda aka sanar da ni shi ne wasu sun ce wajen sana’arsu aka je aka far musu, wasu kuma sun ce har gida aka je suna barci aka kona musu gidan, wasu kuma sun ce harbe su aka yi. Allah ne kadai Ya san ainihin yadda abin ya faru.”

Salame ya ci gaba da cewa, “Ranar Litinin da dare ne abin ya faru kuma sunayen wadanda aka kashe su ne Abdullahi Mamman da Hauwa’u Ibrahim da Malam Muhammadu da Murtala. Abdullahi Mamman da Hauwa’u mata da miji ne.”

Sha’aibu Salame ya ce, “Mutanen sun shafe sama da shekara 30suna zaune a garin tun ana zuwa a kore su, su gudu idan kura ta lafa su koma su ci gaba da harkokinsu.”

Sai dai Salame ya ce akwai ragowar mutanen da suke zaune a gidan da suka tsira da ransu.

Ya ce, “Gawarwakin an kwashe an kai su Anaca domin yin jana’izarsu a can.”

Dan uwan mamatan ya ce suna zargin masu fafutukar kafa kasar Biyafara ne wato IPOB suka aikata wannan ta’addanci .

Sha’aibu Salame ya yi kira ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya sa baki a kan lamarin.

“Ya kamata Gwamna Tambuwal ya sa baki wajen yi wa Gwamnan Jihar Anambra magana ya biya diyyar rayukan da aka kashe,” in ji shi.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra amma hakarsa ba ta cim ma ruwa ba.

Aminiya ta nemi jin ta bakin mutanen garin Salame a Jihar Sakkwato, inda suka tabbatar da kashe musu mutane a Anambra.

Wani mai suna Abdullahi Salame ya ce, “Mun samu labarin kashe mutanenmu a Anambra, sannan har yanzu akwai wasu mutanenmu da ba a samu labarinsu ba.

“Yanzu haka muna zaman makokin mamatan ne a nan Sakkwato. Muna kira ga gwamnati ta kwato mana hakkin ’yan uwanmu da aka kashe,” inji shi.