✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka rantsar da Shugaban Amurka Joe Biden da Kamala Harris

Kamala Harris ta zama mace ta farko Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka

Shugaban Kasar Amurka na 46, Mista Joe Biden da Maitaimakiyarsa, Kamala Harris, sun karbi rantsuwar fara aiki tare da a wa’adin mulkinsu na shekara hudu.

Kamala Harris, wadda ’yar asalin nahiyar Asiya ce ta zama mace ta farko Mataimakiyar Shugaban Kasa a tarihin Kasar Amurka wadda dimokradiyyarta ta shekara 244.

Jawabin Joe Biden

Yayin da hankalin duniya ya koma ga sabuwar gwamnatin, sabon shugaban kasar, ya yi alkawarin kyautata alakar Amurka da kasashe, “ba na baya ba kadai, na yauzu da kuma nan gaba.”

A jawabin nasa na bayan karbar rantsuwa, Biden ya ce “ku dauki kalamaina a matsayin alkawari,” cewa zai kare daukacin ’yan kasar har da ’yan adawa kamar magoya bayansa.

Joe Biden yan karbar ratsuwar fara aiki

Sabon shugaban kasar ya ce Amurka ta cancanci fiye da matsayinta na yanzu, ya ce gwamnatinsa za ta dage wurin magance mamayar da fararen fata ke yi da kuma ta’addanci a cikin kasar.

Ya yi kira ga ’yan kasar da su hada kai, yana mai cewa da hakan kasar za ta yi nasara yakar annobar COVID-19 da ta kashe mutum 400,000 a kasar.

A cewarsa, yanzu lokaci na gyara, hada kan al’ummar kasar, kawo sauye-sauye da ingata al’amura Amurak da kuma cimma muradunsu.

Da yake cewa yin adawa ’yanci ne na kowa, Biden ya kuma yi kira ga al’ummar kasar da su jingine bambance-bambancensu domin daukaka ta da kuma magance matsalolinta.

Ya kuma yi jinjina ga iyayen da suka kafa kasar da jama’ar kasar da suka bayar da gudunmuwa wurin kare kasar.

Trump ya kaura ce wa taron

Tsoffin Shugabannin Amurka da matayensu sun halarci taron da ake girke adadin jami’an tsaro mafi yawa a tarihin bikin rantsar da shugaban kasar Amurka.

Joe Biden yan karbar ratsuwar fara aiki

Tsoffin Shugabannin da suka halarci taron sun hada da George Bush da Barrack Obama wanda Mista Trump ya gada da kuma Bill Clinton tare da matarsa Hillary ta kara da Trump a zaben da Trump ya kayar da ita ya zama Shugaban Kasa na 45.

Shahararriyar mawakiyar kasar Amurka, Lady Gaga ce ta yi taken kasar, ’yan mintoci kafin rantsar da sabbin Shugabannin Kasar.

Taron bikin taron wanda aka takaita yawan mahalartansa shi ne wanda aka girke adadin jami’an tsaro mafi yawa a tarihin bikin rantsar da shugaban kasar Amurka.

An gudanar da shi nea gaban Ginin Majalisar Dokokin Amurka, Capitol, inda a mako biyu da suka gabata magoya bayan Shugaba kasar mai barin gado, Donald Trump suka yi tarzoma.

Magoya bayan Shugaba Mai Barin Gado, Donald Trump sun yi hargitsin ne don hana Majalisar Dokokin Kasar tabbatar da zaben Biden da Kamala da kuma ba su shaidar cin zabe.

Trump dai ya kirayi magoya bayansa su yi tattaki zuwa Majalisar ne saboda ya tsaya kai da fata cewa an murde sakamakon zaben da ya nemin yin tazarce ne.

Mista Trump, wanda Mataimakinsa Mike Pence ya halartar taron dai ya riga ya ki halartar taron.