✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake bikin rufe Gasar Rubutattun Wakokin Hausa a Sakkwato

Za a kammala bikin da misalin karfe biyu na rana.

A yau Laraba ake gagarumin bikin rufe Gasar Rubutattun Wakokin Hausa da ake gudanar wa a Jihar Sakkwato.

Sashin Hausa na Jami’ar Usman Danfodiyo ya shirya dangane da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Tun da farko dai jami’ar ta saka gasar ce a Janairun bara, inda aka gayyaci marubuta wakokin hikima su rubuta waka wadda ta danganci al’amuran tsaro a Arewa.

Jami’in Kwamitin gasar, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai ya shaida wa wakilinmu cewa mawaka sama da 100 suka shiga gasar daga sassa daban-daban na Najeriya.

Ya ce cikin mawakan sama da 100, an tace mutum 30, wadanda suka fafata a zagaye na karshe, inda kuma a yau ake bikin rufe gasar, inda za a karrama zakaru daga na daya zuwa na uku.

Haka kuma, an gudanar da gasar tsarin wakar Ga-ni-ga-ka, inda aka ba mawaka maudu’in su rubuta waka mai baitoci 10 a kan Zaman Lafiya cikin minti 20.

A nan take aka kammala kuma ‘yan takara sama da 40 suka fafata. Su ma a yau za a sanar da zakaru uku da suka yi zarra.

A yayin rufewar, za kuma a gabatar da gasar Ja-in-ja, inda mawaka za su kalubalanci juna da baitoci kai tsaye a gaban jama’a.

Taron dai yana gudana ne a babban zauren taro na Jami’ar Usman Danfodiyo Sakkwato.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal shi ne Babban Mai Masaukin Baki.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Sarkin Yamman Sakkwato, Shugaban Kwamitin Tsaro a Majalisar Dattijai ta Najeriya shi ne Babban Bako.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Mai martaba Sarkin Yauri, Dokta Muhammad Zayyanu Abdullahi su ne Ubannin Taro.

Shugaban Taro kuma shi ne Mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, a yayin da Dokta Aliyu Usman Tilde shi ne Bako Mai Jawabi.

A yayin da kuma Shugaban Jami’ar Usman Danfodiyo, Farfesa Lawal Sulaiman Bilbis ya kasance Mai Masaukin Baki.

Ana sa ran za a kammala bikin da misalin karfe biyu na ranar yau ta Laraba.