✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake dafa-dukar shinkafa da daddawa

Shinkafa ta zama abinci gama-gari, amma hanyoyi daban-daban da ake da su na dafa masu gamsarwa, wata shinkafar ta fi wata. Ba maganar tuwon shinkafa…

Shinkafa ta zama abinci gama-gari, amma hanyoyi daban-daban da ake da su na dafa masu gamsarwa, wata shinkafar ta fi wata.

Ba maganar tuwon shinkafa da ko fara da miya ba, a’a, dafa-dukanta abinci ne da kwatancensa kadai, tun kafin ka ji kamshinsa, zai sa yawun mutum ya tsinke.

An yau mun kawo muku tsarabar wata shinkafa dafa-duka ta musamman, wadda ake yi da daddawa.

Abubuwa da ake bukatar

 • Shinkafa
 • Tumatiri
 • Attarugu
 • Daddawa
 • Kifi
 • Man ja
 • Shuwaka
 • Albasa

Yadda ake hadawa

 • A dora tukunyar da ruwa a cikinta har sa ya tafasa
 • sannan a dauko shinkafa a wanke a zuba a ciki,
 • Idan ta dan tafasa kamar na minti 15 sai sauke a wanke da ruwa
 • A yi jajjagen tumatir da attarugu da albasa da citta a ajiye a gefe
 • Sai a wanke shuwakan da gishiri domin dacin ya fita
 • A dora tukunyar a wuta a zuba manja a yankakken albasa a zuba ta soyu sosai
 • Daga nan sai a zuba kifi ya soyu a kwashe kifin a zuba daddawa ya soyu
 • A zuba jajjagen kayan miyar a ci gaba da soya shi
 • A sa ruwa da sinadarin dandano da gishiri da kayan kamshi da shinkafar
 • Daga nan sai a gauraya a rufe tukunyar na kamar tsawon minti 45
 • Idan ta fara nuna sai a dauko wankeke shuwaka a zuba na tsawon minti
 • Idan ya nuna sai a gauraya  a sauke

A ci dadi lafiya.