✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake dahuwar shinkafa ’yar Senagal da kifi

Kayayyakin da ake bukata Shinkafa Karas Koren wake da tattasai Tattasai Attarugu Albasa Nikakken nama Sinadarin dandano Kori Tafarnuwa Citta Kifi Yadda ake girka Kalwale…

Kayayyakin da ake bukata

Shinkafa

Karas

Koren wake da tattasai

Tattasai

Attarugu

Albasa

Nikakken nama

Sinadarin dandano

Kori

Tafarnuwa

Citta

Kifi

Yadda za a girka shinkafar

  • A dora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa.
  • A dauko shinkafa a wanke a zuba a ciki.
  • Idan ta dan tafasa kamar na minti 10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa, a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
  • Daga nan sai a  samu danyen nama a nika shi.
  • A sake dora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyada a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai.
  • Sannan sai a zuba nikakken naman a ciki a ci gaba da soya shi.
  • Daga nan kuma sai a dauko citta da tafarnuwa da sinadarin dandano da kori sai a ci gaba da juya su, sannan a zuba su karas da koren waken da tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da murfi na tsawon minti 20, sannan a sauke shi.
  • Sai a wanke kifi a ajiye shi.
  • A zuba man gyada  a tukunyar ya yi zafi, sai a soya kifi a ciki har sai kifin ya fara canja kala zuwa ruwan kasa kafin a cire ci daga wuta.