Yadda ake Dashishi | Aminiya

Yadda ake Dashishi

  Rahima Shehu Dokaji

Dashishi abincin gargajiya ne da ke kara lafiya, kuzari, da kuma gina jiki.

A yau shi ne abin da muka yiwo muku tsarabar yadda ake girkawa.

Kayan da ake bukata:

 • Alkama kofi 8
 • Mai kofi 1
 • Gishiri kadan
 • Ruwa

Yadda ake yi:

 1. Ki sami alkama ki tsince ta sai a surfeta a cire dusar.
 2. A wanke ta, a bari ta bushe, sai a nika a barzo ta amma kada ta yi gari sosai.
 3. A zuba ruwa a tsame ta yadda barjin zai yi laushi idan an turara shi, sai a tsame.
 4. A sami madanbaci a turara shi, har sai ya fara cuccurewa,
 5. Daga nan sai a zuba mai da gishiri a juya sosai amma a sauke.
 6. Sai a sa mai yadda zai warware, a kara mayarwa shi kan wuta.
 7. Idan ya yi za a ji yana kamshi, sai ci.

Ana ci da miyar taushe ko miyar ganye ko duk miyar da ake so.