✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake Faten Doya

Uwargida barka da rana. Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo yadda ake girka Faten Doya. Ga kayayyakin hadin da ake bukata:…

Uwargida barka da rana. Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo yadda ake girka Faten Doya.

Ga kayayyakin hadin da ake bukata:

Doya

Manja

Alayyahu

Kifi (Cray fish)

Albasa

Attarugu

Tumatir

Kifi

Nama

Tafarnuwa

Citta

to dandano

Yadda za a hada

A sami danyar doya a fere ta a yayyanka ta kanana-kanana, sannan a wanke a ajiye a gefe.

A zuba nama a tukunyar da albasa da gishiri har sai sun yi laushi.

A dora  tukunya a wuta a sai zuba manja sanan a zuba yankakkiyar albasa da dakakke tumatir, attarugu, tafarnuwa da citta.

A yi ta gaurayawa har sai sun soyu.

Sai a zuba nama da romo da maggi.

A wanke kifi da crayfish a saka su, idan ya dan tafasa sai a dauko yankakkiyar doya a zuba a ciki har ta dahu ta yi laushi

Sai a samu ganyen  alayyahu a yayyanka shi a wanke da ruwan gishiri sai a zuba  a ciki

Idan ya nuna sai a gauraya a sauke.

[Idan an lura  za a ga yawancin girke-girkenmu akwai  tafarnuwa a ciki saboda tana magani sosai a jiki kuma tana fitar da kamshi a cikin abinci]