✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake faten wake mai alayyahu

Kayan hadi Wake Manja Attarugu Tafarnuwa Albasa Tumatiri Gishiri Sunadarin dandano Alayyahu Yadda ake hadin A gyara waken a sa a cikin tukunya sannan a…

Kayan hadi

  • Wake
  • Manja
  • Attarugu
  • Tafarnuwa
  • Albasa
  • Tumatiri
  • Gishiri
  • Sunadarin dandano
  • Alayyahu

Yadda ake hadin

A gyara waken a sa a cikin tukunya sannan a zuba ruwa a dora a wuta, sai waken ya yi kaman minti 45.

A samu ganyen alayyahu a yayyanka a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe.

A yi jajjagen tumatiri, albasa, attarugu da tafarnuwa.

Bayan wake ya fara laushi, sai a  sauke shi a wanke da ruwa a ajiye a gefe.

Daga nan sai a soya manja da albasa a tukunyar sannan a zuba jajjagen kayan miyar a  ciki.

Bayan ya soyu sai a zuba wake da sunadarin dandano da gishiri a ruwan su dahu.

Idan waken ya fara laushi sosai sai a zuba yankakken alayyahu ya yi kamar minti uku zuwa hudu.

Daga nan sai a gauraya a sauke tukunyar.

Za a iya cin wannan girki shi kadai ko a hada da burodi ko garin kwaki.

Dabarun girki

  • Idan abinci ya yi gishiri da yawa, a yayyanka dankali mitsi-mitsi a saka a ciki, anjima sai a cire shi, zai rage gishirin.
  • Idan abinci kamar miya ta fara tsami, a sa baking foda da kayan dandano a ciki kafun a dumama.