✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake fifita ‘sharholiya’ a kan ilimi a Najeriya

Yadda ake fifita masu harkar sharholiya fiye da zakakuran masu ilimi a Najeriya.

Harkar ilimi a Najeriya ya shiga wani hali, ganin yadda gwamnatoci da wasu daidaikun mutane suka fi nuna kula da karramawa da kuma fiffiko ga masu harkokin nishadi a kansa.

Yadda aka daukar nayin masu yin irin wadannan abubuwa na nishadi a gidajen talabijin da sauransu fiye da yadda suke bayarwa ga wadanda suka yi fice a fannin ilimi, ya janyo korafi musamman a tsakanin masana ilimi.

Hakan ya biyo bayan fara shirin Big Brother Naija karo na shida a bana, wanda aka fara a ranar Asabar da ta gabata, inda aka ware akalla Naira miliyan 90 a matsayin kyaututtukan da za a bai wa zakarun shirin.

Wannan ya sa wadansu ’yan Najeriya suke tambayar me zai hana gwamnati ta mayar da hankalinta kan fifita dalibai da suka yi fice a fannnonin ilimi maimaikon fannin sharholiya?

Wadansu masana suna ganin kamata ya yi gwamnati ta mika wannan zunzurutun kudi da ta ware domin inganta fannin ilimi ko a yi amfani da kudin wajen tallafa wa masu bincike da kirkire-kirkire kamar daliban da suke sakandare da manyan makarantu.

Kyaututtukan ban-mamaki ga zakakuran daliban ilimi

Wadansu daga cikin daliban da suka yi fice a jami’o’in kasar nan an yi musu kyaututtukan da suka bai wa mutane mamaki inda suka kama daga bayar da kwayar doya da Naira 200.

An yi ta yada hoton wani dalibi da ya yi zarra a Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOU) da aka bai wa doya da kaza a matsayin kyauta bayan nasarar da ya samu a makarantar wanda hakan ya sa ake ganin ana nuna rashin kula ga masu ilimi manyan gobe.

Akwai labarai da yawa da aka samu inda aka bai wa dalibai da suka yi zarra a karatu kyaututtukan da suke nuna halin-ko-in-kula, cikinsu har da Bamisaye Tosin, wacce aka bai wa Naira 200 a matsayin Gwarzuwar Daliba a fannin Kula da Gine-Gine a Jami’ar Jihar Ekiti (EKSU).

A Jami’ar Ibadan ta Jihar Oyo an bai wa daliba Oluwole Hikmat Ibrahim-Buruji kyautar Naira 2,000 a matsayin Gwarzuwar Daliba a fannin Ilimin Larabci da Addinin Musulunci a shekarar 2016.

Dalibar da ta yi zarra a fannin Koyon Aikin Jarida a Jami’ar Ilorin, Durawaiye Gbemisola ta ce ita an ba ta kyautar Naira dubu 10 ne a maimaikon sauran da aka yi musabaha kawai da su.

Ta ce duk da cewa ba kudin ne a gabanta ba, sai ta nemi a rika bai wa dalibai tallafin karatu ga duk wanda ya nuna gwaninta domin kara musu karfin gwiwa.

Wadansu dalibai da suka yi zarra a wasu lokutan, kyautar kwamfuta ake ba su ko kuma kawai a yi musu tafi kawai.

Sai dai labarin ba haka yake ba a fannin ’yan wasa ko nishadi, inda ake ba wadanda suka yi nasara ko wadanda suka shiga gasar kyauttuka masu yawa daga kudi zuwa sauransu ciki har da motoci da gidaje da tikitin jirgi na tafiye-tafiye zuwa kasashen waje da sauransu.

Binciken da Aminiya ta yi ta gano cewa akwai rata babba a irin kyaututtukan da ake bai wa wadanda suka yi nasara a fannin sharholiya da na sashin ilimi, inda masana ilimi suka nuna bai dace ba, idan aka yi la’akari da gudunmawar da bangaren ilimi ya bayar ga ci gaban kasa.

A cikin dalibai 21 da suka shiga wasu gasanni takwas kan ilimi da aka yi a kasar nan daga shekarar 2018 zuwa 2020 an kiyasta kyaututtuka da suka samu a kan sama da Naira miliyan 35 ne kawai.

Daliban da suka zo na daya da na biyu da na uku a gasar rubutu da Gidauniyar Ilimi ta Bankin UBA ta shekarar 2020, tallafin karo ilimi na Naira miliyan 6 aka ba su.

A shekarar 2019 zakarun gasar lissafi ta makarantun sakandare da Gidan Talabijin na Kasa da Kamfanin Cowbellpedia ke shirya wa ’yan karama da babbar sakandare kyaututtukan Naira miliyan 9 aka raba musu. An kuma bai wa zakarun damar yin tafiye-tafiye zuwa kasar waje.

A karshen gasar da Hukumar Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya (NSE) ta shirya wa ’yan sakandare, dukkan zakarun an ba su Naira dubu 950 ne, sai tallafin zuwa jami’o’i da kuma Naira miliyan 1 da dubu 250, na hannun jari da kwamfutar hannu.

Haka kuma gasanni biyu da aka shirya na karatun haruffa da hada baki ta kasa a shekarar 2019 zakarun gasar sun samu tallafin Naira miliyan biyu ne da dubu 200 a matsayin kyauta.

Shi ma zakaran gasar fasahar sadarwa (ICT) a shekarar 2018 ya samu kyautar Naira dubu 250, da Naira dubu 150, tallafin karo ilimi sai kwamfuta da wasu kyaututtuka.

Gasar fannin kimiyya ta Interswitch SPAK, zakarunta sun samu tallafin karo ilimi a jami’o’i na Naira miliyan 12.5 da alawus duk wata sannan da kwamfutocin hannu.

Daga cikin manyan gasannin da ake yi a kasar nan akwai wanda Kamfanin NNPC yake shiryawa inda zakarunta a shekarar 2018 suka samu tallafin Naira dubu 750 a duk zangon karatu, kuma zakarun shiyyoyi suka samu tallafin karatu na Naira dubu 100 bai-daya.

Jimillar kudin da aka bayar na tallafin karatun ya kama Naira miliyan 1 da dubu 350.

Zakaru uku na gasar PZ Cussions Chemistry a shekarar 2019, sun samu Naira miliyan 2 da dubu 250 da wasu kyaututtuka na tagulla sannan za a rika aika musu da sabulan wanka na tsawon shekara daya.

Maitaimakin Kwanturola mai Kula da Hulda da Jama’a na Cibiyar Lissafi ta Kasa da take Abuja, Dokta Onyekachi Njoku ya ce zakarun gasar lissafi da suka shirya sun samu shiga wasu daga cikin jami’o’in da suka yi fice a duniya da suka zaba da kansu.

Sannan ya ce an ba su kyautar tagulla da satifiket. Kuma ya ce “A matsayinmu na gwamnati ba za mu so fadin yawan kudin ba. Amma dai cibiyar ta ba su kyautar kudi amma ba zan iya fadi ba.”

Kyaututtukan da ake samu a sharholiya

Manyan kyaututtuka da aka bai wa zakarun sharholiya na talabijin na gasar Naija Tops.

Zakaru shida na gasannin da aka nuna a shekara, kusan Naira miliyan 83 sannan aka ba su kyaututtuka.

A shekarar 2019 zakaran gasar shirin Big Brother ya samu kyautar Naira miliyan 30 da wasu kyaututtuka da aka kiyasta kudinsu zai kai Naira miliyan 30.

Gasannin sharholiya irin wadannan sun zama hanyar ficewa daga talauci ga mafi yawan ’yan Najeriya.

A duk shekara zakarun wadannan gasanni da wadanda suka shiga gasar sukan koma gida da kyaututtuka na miliyoyin Naira.

Hakan ya sa matasa suke tururuwar shiga irin wadannan gasanni a lokacin tantancewa.

Zakaran BBnaija, Michael Efe Ejeba, a shekarar 2017 ya tafi gida da zunzurutun kudi har Naira miliyan 25 sai Miracle Igbokwe wanda ya ci gasar a shekarar 2018 da ya samu kyautar Naira miliyan 25 da sauran kyaututtuka da aka kiyasta sun kai Naira miliyan 45.

An kara yawan kudin da ake bayarwa da Naira miliyan biyar, inda Mercy Eke ta tafi da Naira miliyan 30 da kuma kyaututtuka na Naira miliyan 30 a shekarar 2019.

A bara Olamilekan Agebleshe wanda ya lashe gasar ya samu kyautar Naira miliyan 30 da kyaututtuka na Naira miliyan 45.

Zakaran gasar 2021 Nigeria Idol Kingdom, Kroseide ya samu Naira miliyan 30 da kyaututtuka na sama da Naira miliyan 20 har da mota kirar SUV.

Wadansu da suke shirya irin wannan gasa ta talabijin da ake kira ‘The Voice Nigeria’ sun kara kyautar kudin da suke bayarwa a shekarar 2021 daga Naira miliyan 7 zuwa miliyan 10 sannan za a hada da mota da wasu kyaututtukan.

Zakaran gasar MTN Yellow Star Naira miliyan biyar ya samu da kuma tallafin karo ilimi a fannin waka.

Zakaran wani shiri da ake gabatarwa a talabijin inda ake koyon girki Knorr Taste Questions Quest shi ma ya lashe Naira miliyan biyar da mota da kayan dafa abinci da sauransu.

Haka wanda ya yi nasara a gasar rawa ta Glo-dance With Peter ya lashe Naira miliyan 3 da mota SUV da sauran kyaututtuka.

Mafi yawan irin wadannan matasa da suka lashe gasannin na sharholiya, rayuwa takan yi musu kyau saboda manyan kamfanoni da gwamnoni suna neman su a jihohinsu don su taimaka wurin yi masu tallan manufofinsu, musamman a lokacin yakin neman zabe sannan akan yi musu kyaututtuka.

A shekarar 2018, bayan ya lashe gasar sharholiya ta BBNaija, Miracle Igbokwe ya samu kyautar Naira miliyan 2 da fili daga Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha.

Sannan a bara, Gwamnan Jihar Bayelsa ya tallafa wa ’yan jiharsa biyu da suka shiga gasar ta hanyar ba su mukaman masu taimaka wa Gwamna.

Laycon wanda ya lashe gasar BBNaija a zango na hudu shi ma ya samu kyaututtuka daga Gwamnatin Jihar Ondo.

An ba shi Jakadan Matasa sannan aka ba shi gida da Naira miliyan biyar.

Sai dai irin wannan karramawa da ake wa irin ’yan wasan sharholiya ba a nuna wa zakarun da suka yi kwazo a fannin ilimi.

Yawancinsu ba su samu irin wannan karramawa ba duk da nasarorin da suke samu.

Mafi yawan lokuta ba a jin doriyarsu bayan an kammala gasar.

Zakaran 2017 na gasar Haruffa, Shariff Muhammad a tattaunawa da shi ya ce cin gasar da ya yi ya ba shi damar fahimtar bukatun da yake son ya cim ma a rayuwarsa.

Ra’ayoyin masana kan sashen ilimi a Najeiya

Tunde Akanji wanda masani ne a fannin ilimi ya nuna damuwar cewa nuna fifiko da ake yi wa sashen sharholiya da nishadi ta hanyar yi musu kyauta ta fitar hankali babban hadari ne ga kasar nan.

Ya ce akwai bukatar Najeriya ta mayar da hankali wajen maido da al’adu da martabarta ta hanyar fahimtar abin da muke son cim mawa.

“Akwai damuwa cewa yanzu al’umma sun fi fifita ’yan sharholiya da nishadi a kan fannin ilimi,” inji shi.

Iyaye sun koka

Wata uwa, Adeola Ayinla ta ce ga dukkan alamu ’yan Najeriya ba su damu da ba da tallafin karo ilimi ba musamman ’ya’yan masu hannu da shuni wanda hakan ya sa suke daukar nauyin irin wadannan wasanni na sharholiya da nishadi.

“Wadansu da suke cikin gwamnati ba su damu da inganta ilimi ba.

“Me kake bukata daga wajen wanda yake gwamnati da ba shi da digiri ko wanda yake je-ka-na-yi-ka.

“Kada ka yi min gurguwar fahimta amma dai sai mai ilimi ne zai san muhimmancinsa,” inji ta.

Amina Bassey ta dora wa gwamnati da iyaye da masu ruwa-da-tsaki ne alhakin abin da yake faruwa.

“Duk yaron da ya ga iyayensa suna kallon irin wadannan shirye-shirye na sharholiya da nishadi maimakon shirin ilimi, zai ki shiga gasar ilimi a makarantansu,” inji ta.

Ilimi yana kan gaba a Najeriya – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sashin ilimi ne a kan gaba a mulkinsa.

Shugaban ya bayyana haka ne ne a ranar Alhamis din makon jiya lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin makarantu masu zaman kansu a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina.

Shugaban wanda ya ce za a kara mai da hankali wajen ci gaban ilimi, ya ce, “Za mu kara kudin da muke ware wa fannin ilimi domin inganta harkar koyarwa a kokari da muke yi na inganta fannin ilimin.”

Shugaban Kasar wanda ya tattauna da dalibai ya nanata musu amfanin biyayya wurin koyon ilimi.

Buhari a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar ya yi kira ga dalibai da kada su cire tsammanin ciyar da kasar nan gaba.