✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ake Gasar Kyan Rakuma A Saudiyya

Za a zabi rakuma da suka fi kyau da iya taku da ado da Gasar Rakuma ta Sarki Abdulaziz, wadda ita ce ce mafi girma…

Garken rakuma daga sassan kasashen Larabawa sun isa kasar Saudiyya domin kece raini a Gasar Kyan Rakuma ta Sarki Abdulaziz kamar kowace shekara.

Tuni dai baki daga sassan duniya suka fara yi wa kasar tsinke, don gane wa idonsu yadda za ta kaya a matakai daban-daban na gasar, wadda ita ce mafi girma a yankin Gabas ta Tsakiya.

Duk safiya ’yan kallo kan halarci filin gasar domin kashe kwarkwatar idonsu, inda a duk mako ake fitar da zakara a rukuni daya, na tsawon mako shida.

Masu rakuma kan shafe watanni suna kiwon su da ba su kulawa ta musamman gabanin fara gasar wadda a karshe za a fitar da gwarazan da suka lashe kambun.

Masu shiga gasar sun bayyana cewa rakuma na bukatar kyakkyawan shiri, kulawa da lafiyarsu da ba su lafiyayyen abinci mai gina jiki, hai da kwalliya da kuma jigilar su.

Masu kallon gasar kyan rakuma a Saudiyya (Hoto: Arab News).
Muhimmacin rakumi a matsayin abin alfahari ga Larabawa ne ya sanya gasar ta yi shuhura, inda ake kawata su da ado na musamman don zabar gwani.

Abubuwan da ake la’akari da su wajen zaben gwarzo sun ha da da kyan siffar rakuma, tsawon wuya, iya taku, kyawun hanci, girman kai, tsayi da kuma ado.

Za a gudanar da gasar ce tsawon makonni shida, a kuma kammala ta a tsakiyar watan Janairu.

Wani shahararren mai rakuma da ke gasar, Falah bin Melhem, ya ce dabbobinsa sun sha shiga gasar, cikin har Mazayen Al-Ibil da aka kammala a baya-bayan nan a kasar Qatar.

Shi kuma Bin Melhem ya ce rakumansa sun sha lashe gasanni, kuma a wannan karon ma yana fata za su samu kyauta a gasar da ke gugdana da kasar Saudiyya.