✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar shuwaka

Assalamu alaikum uwargida! Barkanmu da sake saduwa  da ke a cikin wannan filin namu na girke-girke. Kamar kullum dai ba zan fasa ba da shawara…

Assalamu alaikum uwargida! Barkanmu da sake saduwa  da ke a cikin wannan filin namu na girke-girke. Kamar kullum dai ba zan fasa ba da shawara cewa miya ita ce sirrin dadin tuwo. Idan har mace ta iya sarrafa miya da iri-iri, lallai kakarta ta yanke saka. Domin maigida ko tafiya zai yi sai ya yi marmarin yin wannan tafiya da ita. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake miyar shuwaka. Tare da fatan za a gwada irin wannan girki don kwarewa a fannin girke-girke.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Ganyen Shuwaka

•        Manja

•        Naman shanu

•        Kayan ciki

•        Kifi banda

•        Danyen kifin karfasa

•        Magi

•        Kori

•        Kifin ‘cryfish’

•        Attarugu

 

Hadi

A kankare fatar danyen kifin karfasa sannan a dora a wuta hade da magi da ruwa sannan a dafa har sai ya yi laushi sosai sannan a sauke. A cire kashin cikin kifin gaba daya, sannan a zuba a turmi a daka shi har sai ya yi laushi sannan a kwashe a ajiye a gefe.

A wanke naman shanu da kayan ciki a dora a kan wuta da gishiri kadan. Sannan a wanke bandar kifi a cikin ruwan zafi a cire kayar kifin.

Bayan naman da kayan cikin sun nuna sannan a zuba su a cikin tukunya tare da bandar kifin da kifin ‘cryfish’ da kuma dakakken kifinkarfasar. Sannan a dora wankakkiyar shuwaka a wuta da jajjagen attarugu da kori.

Sannan a gauraya su a zuba magi da manja. Idan ganyen shuwakar ya nuna sai a sake gauraya girkin a sauke. Za a iya hada wannan irin miyar da kowane irin tuwo.

A ci dadi lafiya!