✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girkin faten acca

Uwargida barka da wanann lokaci a wannan filin na girke-girke. Ina fatar ana gwada irin girke-girken da muke kawo muku. Yana da kyau a rika…

Uwargida barka da wanann lokaci a wannan filin na girke-girke.

Ina fatar ana gwada irin girke-girken da muke kawo muku.

Yana da kyau a rika sauya girki kayatar da iyali da kuma Karin dandano.

A yau na zo muku ne da yadda ake yin faten acca.

  • Kayan hadi:
  1. Acca
  2. Ruwa
  3. Allayahu
  4. Lawashin albasa
  5. Albasa
  6. Attarugu
  7. Magi
  8. Gishiri
  9. Kori

 

  • Yadda ake hadawa
  1. A dora tukunya a wuta sannan a sanya acca daidai bukata a ciki idan ruwan ya yi zafi.
  2. Kar a saka acca da yawa saboda idan ta fara tafasa tana yin kauri.
  3. Sai a zuba yankakakkiyar albasa, alayyahu, lawashi da attarugun a ciki a juya.
  4. Bayan nan sai a zuba magi, gishiri da kori daidai bukata a juya sosai.
  5. Daga nan sai a bar shi a wuta ya dan turara kadan kafin a sauke.

Asha dadi lafiya.

Mulahaza: Sannan a rufe tukunyar har sai ya fara tafasa.