Yadda ake girkin Gas Meat | Aminiya

Yadda ake girkin Gas Meat

  Amina Abdullahi

Barkanmu da warhaka, a yau na kawo muku yadda ake girki mai suna Gas meat. 

Ana sayar da wannan gasasshen nama kusan ko’ina. Amma ba a san yadda ake sarrafa shi ba.

Ya kamata a yi wa maigida irin wannan gashi domin sanya kunnensa motsi.

– Kayan hadi

 •        Naman rago (ba mai kitse ba)
 •        Albasa 5
 •        Garin kuli-kuli
 •        Garin citta
 •        Man gyada
 •        Gishiri
 •        Magi
 •        Curry
 •        Thyme

– Yadda ake hadin

Bayan an wanke nama sai a yanka shi sala-sala, a yanka albasa ita ma sala-sala.

A dora naman a tukunyar da ake suyar kosai, sai a rufe a jira na tsawon minti 20.

Bayan naman ya nuna da ruwan jikinsa, sai a fara gauraya shi da cokalin girki.

Sannan a zuba yankakkiyar albasa da dakakken kuli-kuli da man gyada da dakakkiyar citta da curry da thyme da gishiri kadan da magi daidai dandanon da ake so.

Sai a yi ta gaurayawa har sai albasar ta nuna, sai a sauke.