✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girkin kaza na musamman

Ki dinga bin mu a shafinmu ne girke-girke domin koyon salo iri-iri.

Assalamu alaikum Uwargida, tare da fatar ana cikin koshin lafiya.

Kowacce mace tana da salon yadda take sarrafa kaza, yana da kyau a koyi salon girka ta da dama.

Don haka a yau na kawo muku yadda ake dahuwar ‘Sweet and Sour chicken’. 

Yin girki iri daya yana da ginsarwa. Idan ba ki so maigida ya gaji da girkinki, ki dinga biyo mu a shafin girke-girke duk mako domin koyon salo daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:

•    Kaza.

•    Gishiri da barkono.

•    Kofi daya na ‘cornstarch’ (za a same shi a manyan kantuna).

•    Kwai 2.

•    Man zaitun.

•    Siga.

•    Cokuli 4 na ‘ketchup’.

•    Ruwan ‘distiled vineger.

•    ‘Soy sauce’ (za a same shi a inda ake sayar da kayan hadin salad).

•    Tafarnuwa.

Hadi:                  

Idan uwargida ta wanke kazarta, sai ta barbada gishiri da barkono.

Sannan ta tsoma kazar a ‘cornstarch’. Sai a kada kwai a sake tsoma kazar a ciki. Sannan a soya kazar da man gyada.

A hada sikari da ‘ketchup’ da ‘distilled vinegar‘ da ‘soy sauce’ da garin tafarnuwa a kwano, sai a kwaba su gaba daya.

Sannan a zuba soyayyar kazar a cikin hadin. Sai a saka a cikin ‘oven’ ta gasu na tsawon minti 15.