✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada ‘Apple Smoothie’

Assalamu alaikum jama’a, yau ma mun sake kawo muku wani sabon abin sha na marmari mai suna Apple Smoothie. An yin sa ne daga tufa…

Assalamu alaikum jama’a, yau ma mun sake kawo muku wani sabon abin sha na marmari mai suna Apple Smoothie.

An yin sa ne daga tufa kuma yana daga cikin abin da mutane da dama ke son sha domin marmari ko tarbar baki ko sana’a.

Ya yadda ake hada shi Apple Smoothie a saukake.

  • Abubuwan hadawa:
  1. Apple (tufa)
  2. Sukari
  3. Lemo
  4. Apple flavor
  • Yadda ake hadawa
  1. Da farko za a wanke tufa guda biyu a bare bayan su a yanka su kanana.
  2. A sa a blender a zuba ruwan lemu daya da rabin kofin ruwa.
  3. A markada shi har sai ya yi laushi sosai.
  4. A tace markaden sannan a zuba sukari da Apple Flavour daidai bukata.
  5. Shi ke nan sai a zuba kankara a ciki sannan a sha.