✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada ‘Fruity Zobo’

Assalamu alaikuma jama’a, yau na kawo muku yadda ake hada Fruity Zobo. Hadin Zobo ne na musamman da za a iya yi domin sha a gida…

Assalamu alaikuma jama’a, yau na kawo muku yadda ake hada Fruity ZoboHadin Zobo ne na musamman da za a iya yi domin sha a gida ko taro ko kuma sayarwa. Ga yadda ake hadawa:

Abubuwan da ake bukata

  • Zobo
  • Sukari
  • Abarba
  • Lemo
  • Gurji (cucumber)
  • Karas
  • Citta
  • Kanumfari
  • Flavor

Yadda ake hadawa

A dora ruwa daidai bukata a tukunya ya tafasa, sannan a saka bawon abarba a ciki.

Sai a dauko gyararren citta da kanunfari a zuba a ciki daidai bukata.

Daga nan sai a sa yankakken gurji da lemo a ciki a bari ya yi ta tafasa na minti 15 zuwa 20.

Bayan nan sai a zuba zobon a ciki tafashehen ruwan a bar shi na tawon minti 15 kafin a sauke.

Idan ya huce sai a dauko ruwan nikakakken karas da abarba da gurji da aka riga aka tace a sanya a ciki.

A tabbata sun niku sosai an kuma tace da kyau. Za kuma a iya yin su daban-daban ko a hade.

Daga nan sai a sanya flavor cikin chokali da sukari juya sosai.

Za a iya sanya inabi ko yankaken gurji a ciki in ana bukata.

Sai a je a saka a fridge a bari ya yi sanyi ko kuma a saya kankara a ciki – gwargwadon bukata.

Wannan shi ne yadda ake hada Fruity Zobo.

A sha Fruity Zobo lafiya.