✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada ‘juice’ din kankana da abarba

Samun abu mai dadi a lokacin bude baki abu ne mai bukata musamman abin sha mai dadi. Baya ga masu sha’awar samun kayan marmari na…

Samun abu mai dadi a lokacin bude baki abu ne mai bukata musamman abin sha mai dadi.

Baya ga masu sha’awar samun kayan marmari na ’ya’yan itatuwa, wasu sun fi son abin sha da aka hada ’ya’yan itatuwa.

Shi ya sa muka kawo muku yadda ake hada ‘juice’ din kayan wadannan kayan marmari, wato abarba da kankana.

Kayan hadi

  • Kankana
  • Abarba
  • Sukari
  • Flavor

Yadda ake hadawa

  1. A samu abarba a wanke sai a yayyanka shi a dora a wuta tare da  sukari, idan ya tafasa sai a sauke
  2. Bayan ya huce sai a yanka kankana a hada da abarbar a markada,
  3. Daga nan sai a tace a zuba flavor daidai bukata
  4. Sai a sa a fridge yayi sanyi