✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada jus din karas cikin sauki

Assalamu alaikum, tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda mutum ke son cin abinci mai dadi, yakan so ya samu abun sha mai…

Assalamu alaikum, tare da fatar ana cikin koshin lafiya.

Kamar yadda mutum ke son cin abinci mai dadi, yakan so ya samu abun sha mai dadi da kayatarwa da zai hada da shi ko ya sha shi haka a matsayin abin marmari.

Don haka a yau na kawo muku yadda ake hada yadda ake hada jus din karas wato ‘carrot juice’.

  • Kayan da za a bukata
  1. Karas
  2. Sukari
  3. Madara
  4. Flavour
  5. Lemon zaki
  • Yadda ake hadawa

Za a wanke karas a fere shi sannan a yanka shi kanana.

Daga nan sai a sanya a blender a markada shi ya yi laushi.

A tace shi sosai yadda ba za a samu gari ko tsaki-tsakin karas ba.

A yanka lemon zakin a matse ruwansa a tace sannan a ajiye a gefe.

Azuba wa tataccen karas din madara da flavor daidai bukata da kuma sukari sai a juya.

Daga nan sai a dauko ruwan lemon a zuba a ciki a motsa.

Shi ke nan sai a sanya hadin a cikin fridge, idan ya yi sanyi a sha shi yadda ake bukata.

Wannan shi ne yadda ake hadda karas juice a takaice.