✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ake Hada Lemon Na’a-Na’a Da Kokumba

Hada wadannan abubuwa biyu a waje guda ba karamin lafiya zai kara wa jiki ba

Gurji, wanda aka fi sani da Kakumba, da Na’a-na’a nau’in kayan abinci ne da suka kunshi sinadarai masu amfani sosai ga lafiyar jikin dan Adam.

Kakumba na dauke da wadataccen ruwa a cikinsa, da ke taimakawa wajen rage kiba da bai wa jiki ruwan da yake bukata.

A hannu guda kuma na’a-na’a na taimaka wa jiki magance matsalolin magwas da kumburin ciki tare da taimaka wa kwakwalwa da kuma hana warin baki na larura.

Kun ga ke nan hada wadannan abubuwa biyu a waje guda, ba karamin lafiya zai kara wa jiki ba.

Kayan hadi:

  • Na’a-Na’a
  • Kokumba
  • Dafaffen sukari/Syrup
  • Filebo

Yadda ake yi:

  1. Da farko a samu Na’a-na’a koriya sosai sai a wanke ta tas.
  2. Sai a markada ta daga nan sai a tace a ajiye ruwan a gefe guda.
  3. A samu Kokumba mara daci a yayyanka ta a markada a tace.
  4. Sai a dafa sukari har sai ya narke ya zama tsararo (syrup).
  5. A juye tattaccen ruwan Na’a-Na’a da na Kokumba a kofi.
  6. Dag nan sai a dauko syrup din a zuba a kan hadin.
  7. A zuba filebo na ruwa, dandanon da ake so, a ciki.
  8. Sai a sa a firiji, ko a jefa kankara a ciki, idan ya yi sanyi sai sha.