✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake Kunun Tsamiya

A wannan mako za mu kawo muku yadda ake Kunun Tsamiya ne.

Assalamu alaikum uwargida. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili namu na girke-girke.

A wannan mako za mu kawo muku yadda ake Kunun Tsamiya ne.

Duk da yake akwai yadda kowa ke sarrafa irin nata Kunun Tsamiyar gwada irin namu ma zai sa a yi gyara ko a ji daban da na kullum.

Za a iya shan wannan kunu da kosai domin Karin kumallo a samu karin armashi.

A sha karatu lafiya.

Abubuwan da ake bukata

• Tsamiya • Sukari • Masoro • Citta • Gero

Hadi

Da farko za a wanke tsamiya sannan a jika ta.

Bayan haka, sai a wanke gero a shanya ya bushe sannan a zuba busashiyar citta da masoro a nika a injin din nika.

Kuma nikan gari za a yi. Bayan an gama, sai a tankade garin.

A dora ruwan tsamiya bayan an tace a tukunya sai a jira ya tafasa sannan a kwaba garin geron da aka tankade kadan a kwano da ruwa kadan sannan a rika gaurayawa ana zubawa a cikin tukunyar ruwar tsamiyar yadda zai yi kauri.

Sannan a sauke. A zuba sukari iya yadda ake so.