✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake magance yamutsewar fata a lokacin sanyi

Akwai abubuwa da dama wadanda idan ana yin su za a rabu da yamutsewar fata.

Yanayin sanyi da hunturu yana janyo yamutsewar fata, don haka yana da kyau a kullum a kasance cikin shafa wa fata mai.

Koda an yi alwalla ne bayan an yi Sallah sai a sake shafa wani man don rage gautsi da yamutsewar fata.

Akwai abubuwa da dama wadanda idan ana yin su za a rabu da yamutsewar fata.

• Man kadanya: Za a iya amfani da man kadanya a fata. A hada shi da man zaitun a rika shafawa. Ko a narkar sai a zuba a man shafawa domin rage warinsa.

• Glycerin: Don magance kaushin kafa za a iya gauraya shi da man basilin sannan a wanke kafa da dutsen goge kafa da ruwan dumi. Bayan haka sai a shafa a tafin kafa sannan a sa safa. Haka za a rika yi domin rage kaushin kafa.

• Man ‘moisturizer’: Yana da kyau a samu irin wannan mai don yana taimakawa wajen gyara yamutsewar fata.

• Ruwan fandesho: Yana da kyau a rage amfani da wannan irin fandeshon, saboda yana feso kurajen fuska. A kasance da sanya kayan ado kadan a fuska.

• ‘Cleanser’: Idan za a yi amfani da ruwan goge fuska a samu wadanda sinadaran ba su da karfi domin yin haka na karfafa yamutsewar fuska.

• Yana da kyau a rika amfani da sabulu da sinadaransa ba su da karfi. Kamar amfani da sabulan jinjiraye wajen wanke fuska.

• A wannan lokaci na sanyi fata na yawan yin duhu yana da kyau a rika yin dilke da kurkum domin taimaka wa wajen haskaka fata a gargajiyance.