✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake miyar Alayyahu

Alayyahu yana kara jini, da saukar da sukari ga masu ciwon suga da kuma taimaka wa wajen narkar da abinci

Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke-girke, ina a yau za mu koyar da yadda ake miyar Alayyahu.

Abubuwan da ake bukata:

  1. Alaiyaho
  2. Dafaffafiyar ganda
  3. Dafaffafen kayan ciki
  4. Dafaffafen kwai (ki bare bawon)
  5. Dafaffafen kifi
  6. Ganyen kori
  7. Albasa
  8. Dafaffen markadadden kayan miya
  9. Tumatir na gwangwani
  10. Kayan kamshi
  11. Sinadarin dandano
  12. Man gyada
  13. Lawashi

Yadda ake hadawa:

  1. Ki gyara Alayyahu, amma ba sai kin yanka ba, sai ki wanke da gishiri ki zuba mishi tafasashshe ruwan zafi ki rufe nadan wani lokaci; Sai ki tace a ajiye a gefe.
  2. Dora tukunya a wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama-sama, sai ki kawo tumatir na gwangwani ki sa ki juya ki soya sama-sama.
  3. Sai ki dauko dafaffafen kayan miya ki zuba a ciki ki juya ki rufe zuwa wani lokaci.
  4. Dauko ganda, kayan ciki, kifi, kayan kamshi, sinadarin dandano ki zuba a ciki ki juya, ki rufe tukunya na dan wani lokaci, sai ki kawo dafaffafen kwan ki sa ki juya.
  5. Ki dauko alayyahun nan ki sa a ciki ki juya, ki kuma kawo ganyen kori da lawashi ki sa ki juya ki dan bar shi ya turaru kadan sai ki sauke.

Ana iya cin wannann miyar da kowane irin tuwo, kamar tuwon shinkafa, da kuskus da dai sauransu. A ci dadi lafiya.