✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake miyar nikakken nama

Za a iya cin miyar da dafaffiyar doya ko farar shinkafa ko wani abin da ake sha'wa

Assalamu alaikum uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya azumi?

Yau na kawo muku yadda ake miyar nikakken nama.

Wajibi ne ga uwargida ta koyi girki iri-iri domin samar wa ’ya’yanta ingantaccen abincin da za su kara musu sinadarai a jikinsu da kuma burge maigida.

Ina kira ga mata da su dage su koyi nau’ukan girki domin akan gaji da cin abinci iri daya.

Kayan hadi

 •  Nama
 • Tumatir
 • Albasa
 • Attaruhu
 • Man gyada
 • Tafarnuwa
 • Citta
 • Sinadarin dandano
 • Kori

Yadda ake yin hadin

 1. A samu jan nama wanda babu kitse a cikinsa, a markada shi a ajiye a gefe.
 2. Sai a yayyanka albasa da tumatir sannan a jajjaga da attaruhu da tafarnuwa.
 3. ِA dora tukunya a wuta, a zuba man gyada kadan a ciki.
 4. A sa albasa da tumatir da garin citta kadan da jajjagen attaruhu da tafarnuwa a yi ta soyawa.
 5. A dauko nikakken naman a zuba a ci gaba da juyawa.
 6. Sai a zuba magi da kori a gauraya.
 7. A rage wuta sannan a rufe na tsawon minti biyu.
 8. Aai a sake budewa a juya har sai ta nuna sannan a sauke.

Za a iya cin wannan miyar da dafaffiyar doya ko farar shinkafa ko wani abin da ake sha’wa.

A ci dadi lafiya.